Turkiyya ta dawo da sufurin jiragen sama zuwa Syria bayan shekara 13

A karon farko cikin shekara 13 jirgin Turkish Airlines dauke da fasinjoji 349 ya tashi zuwa Damascus daga birnin Santanbul na Turkiyya

Turkiyya ta dawo da sufurin jiragen sama zuwa Syria bayan shekara 13

Kamfanin jiragen sama na kasar Turkiyya, Turkish Airlines ya dawo da jigilar fasinjoji zuwa Damascus, babban birnin kasar Syriya bayan shekara 13.

Kamfanin dillancin labaran Turkiyya, Anadolu, ya ruwaito cewa a safiyar Alhamis jirgin Turkish Airlines dauke da fasinjoji 345 ya ya sauka a birnin Damascus na Syria daga birnin Santanbul na Turkiyya. Shugaban kamfanin jiragen Bilal Eksi da wasu jami’ansa na daga cikin ’yan rakiya a jirgin.

Anadolu ya ruwaito daya daga cikin fasinjojin mai suna Ahmet Kiraz, wadda ta barko Damascus tun shekara 2012 na cewa, “ina ji akmar a mafarki,” za ta koma Damascus.

Wani jami’in Turkish Airlines ya shaida wa Anadolu cewa nan gaba kamfanin zai kara yawan sawayen da zai yi tsakanin Damascus da Santanbul manyan biranen a kasashen biyu makwabtan juna.

Anadolu ya ruwaito cewa rabon Turkish Airline ya yi jigilar fasinja zuwa filin jirgin kasa da kasa na Damascus, tun watan Afrilun shekarar 2012.

Turkiyya ita ce kasar da ta karbi bakuncin ’yan gudun hijirar Syria mafi yawa a duniya, inda ta karbi bakuncin ’yan Syria miliyan uku bayan barkewar yakin basasa a zamanin tsohon shugaban kasar Syria, Bashal al-Assad.

Tun bayan hambarar da al-Assam wabda a yanzu yake zaman mafakar siyasa a Rasha, dubban daruruwan ’yan Syria da suka yi hijira zuwa wasu kasashe suke ta komawa kasarsu.

A shekarar 2011 bayan yakin basa ya barke a kasar Syria, makwabciyarta Turkiya ta dakatar da sufurin jirage kai tsaye zuwa Damascus.