Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

Babban dalilin da ya sa wasu ke yin laifi shi ne yunwa. Miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da yunwa sakamakon wasu dalilai kamar hauhawar farashin kayayyaki

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

Sakataren Jam’iyyar Leba (LP) na ƙasa, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ce jam’iyyar ta damu matuƙa kan turmutsitsin da ya janyo asarar rayuka kusan 65 da suka haɗa da ƙananan yara, a jihohin Oyo da Anambra da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Alhaji Ibrahim ya ce, turmutsutsun sun yi yawa sosai, yana mai cewa yawan asarar rayuka da aka yi a daidai lokacin da Najeriya ba ta fuskantar wata ibtila’i na nuni da cewa yunwa na iya zama annoba mafi muni da mutane za su iya fuskanta.

Ibrahim, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce kuma talauci ne ke sa wasu ‘yan Najeriya ke ɗibar mai a wuraren haɗarin tanka wanda sakamakon hakan za a samu tashin gobara da ya janyo asarar ɗaruruwan rayuka.

Ya ƙara da cewa binciken da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta gudanar ya nuna cewa sama da mutane miliyan biyu aka yi garkuwa da su a Najeriya a cikin shekara ɗaya kuma ‘yan Najeriya sun biya dala biliyan 1.42 ga masu garkuwa da mutane a cikin lokaci guda.

“Babban dalilin da ya sa wasu ke yin laifi shi ne yunwa. Miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da yunwa sakamakon wasu dalilai kamar hauhawar farashin kayayyaki da rashin tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.

“Sake fasalin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu ya jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalun da babu su ba. Yunwa tana rikiɗewa zuwa annoba kuma mutane da yawa ba za su iya tsira daga wannan yanayin ba,” inji shi.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara