Turmutsutsun karbar tallafi a Nijar ya sa mutum 20 sun mutu

A kalla mutum 20 ne suka rasu wasu yayin da 12 kuma suka samu rauni a wani turmutsutsu wajen amsar taimakon da gwamnan jihar Borno ya kai wa ‘yan gudun hijira a jamhuriyar Nijar. Hakan ya faru ne da safiyar Litinin inda mutane suka yi dandazo a gidan raya al’adu da wasanni na samari da […]

Turmutsutsun karbar tallafi a Nijar ya sa mutum 20 sun mutu

Gwamna Zulum a Nijar

A kalla mutum 20 ne suka rasu wasu yayin da 12 kuma suka samu rauni a wani turmutsutsu wajen amsar taimakon da gwamnan jihar Borno ya kai wa ‘yan gudun hijira a jamhuriyar Nijar.

Hakan ya faru ne da safiyar Litinin inda mutane suka yi dandazo a gidan raya al’adu da wasanni na samari da ‘yan mata MJC da ke garin Diffa.

Gidan na cikin wurare biyu da aka kebe domin raba taimakon da gwamnan jihar Bornon Umara Zulum, ya kai wa ‘yan gudun hijirar Najeriyar a kalla su dubu 12 ke zaune a jihar Diffa.

Wata majiya ta kusa da asibitin Diffa ta ambato mutum 20 mafiya yawan su mata da yara da kuma tsofafi ne wannan lamari ya rutsa da su, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.

Yayin da wasu mutum 12 suka yi rauni lokacin turmutsutsu.

‘Yan gudun hijirar Borno a Nijar

 

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa