Tururuwar sauya sheka da tafarkin dimukradiyya

Tun bayan shan kayin da jam’iyya mai mulki ta PDP ta yi musamman a zaben shugaban kasar watan jiya, ake ci gaba da samun dimbin ’yan siyasar da ke sauya sheka zuwa jam’iyyar da ta yi nasara wato APC. Daga shiyyar Kudu-maso-Yamma da kuma shiyyar Arewa, har ila yau, an samu tururuwar masu sauya sheka […]

Tururuwar sauya sheka da tafarkin dimukradiyya
Tururuwar sauya sheka da tafarkin dimukradiyya

Tun bayan shan kayin da jam’iyya mai mulki ta PDP ta yi musamman a zaben shugaban kasar watan jiya, ake ci gaba da samun dimbin ’yan siyasar da ke sauya sheka zuwa jam’iyyar da ta yi nasara wato APC. Daga shiyyar Kudu-maso-Yamma da kuma shiyyar Arewa, har ila yau, an samu tururuwar masu sauya sheka a shiyyar Kudu-maso-Kudu da kuma Kudu-maso-Gabas. Manyan ’yan siyasa suna jagorantar magoya bayansu a jam’iyyar PDP wajen ketarawa zuwa APC. 

Ana ganin cewa tsoron ’yan siyasa na kasancewa wadanda ba a dama da su shi ne ya haddasa hakan. Wannan ne karo na farko da jam’iyyar adawa ta karbe mulki daga jam’iyyar da take mulki ta hanyar zabe tun bayan samun ’yancin kan kasar nan. Amma batun sauya shekar yana nuni da yadda ’yan siyasa ba su da akida musamman daga bangaren masu barin jam’iyyar PDP. A karkashin mulkin dimukradiyya, ana kafa jam’iyyu ne ba wai domin su kasance su ne masu mulki ba har abada; wannan ne ya sa ake gudanar da zabuka domin zaben mutanen da jama’a ke ra’ayi.
Mulkin dimukradiyyar da ya samu ci gaba shi ne wanda yake bai wa kowa ’yanci zaben abin da yake ra’ayi, ba tare da wani shamaki ba, har ila yau shi ne wanda jam’iyyu daban-daban ke samun nasara a tsakaninsu bayan gudanar da zabuka da jama’a suka kada kuri’unsu.
Nasarar da jam’iyyar APC ta samu ba tana nufin daidaicewar mambobin jam’iyyar PDP ba ne, wacce a yanzu take bukatar kara gina kanta a sabon matsayinta na ’yar adawa da kuma kasancewarta na wani zabi idan masu kada kuri’a sun yi ra’ayinta a nan gaba.
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, ya ce idan abin da ke faruwa ya ci gaba ba tare da daukar wani mataki ba, to zai mayar da kasar nan wata kasa da ke bin tafarkin jam’iyya daya tilo; Farfesa Umaru Pate na Jami’ar Maiduguri ya ce sauya shekar da ke faruwa kamar ruwan dare zai iya kawo karshen siyasar adawa a kasar nan. Wannan ya kara karfafa tsoron kada kasar nan ta fada sahun kasashe masu bin jam’iyyar siyasa daya tilo. An taba bayyana irin wannan tsoron lokacin da tauraruwar jam’iyyar PDP ke haskawa, inda shugabanninta suke bugun kirjin cewa ita ce jam’iyyar da ta fi girma a nahiyar Afirka da kuma cewa za ta ci gaba da mulki har tsawon shekaru 60. Jam’iyyar APC da kuma yadda ta nuna karbuwarta a zaben da ya gabata ya taka wa wancan ikirarin birki, domin yanzu ba jam’iyyar ba ce take mulki a matakin gwamnatin tarayya.
Galibin wadanda suke tururuwar sauya shekar sun yi hakan ne saboda yadda wasu jam’iyyu ba su da manufofi jam’iyya wadanda ake bukatar mambobin jam’iyyar su bi. Abin da yake jawo jama’ar kasar nan sauya jam’iyya galibi ba ya wuce kwadayin samun wani mukami ko iko, ko domin neman daukaka da kuma neman arziki da ke tattare da hakan. Bauta wa jama’a ko kasa, kalamai ne da ake yawan fadi amma ba tare da yin aiki da su ba.
’Yancin mu’amala da kowa da kundin tsarin mulkin kasar nan ya bayar ya hada da ’yancin kasancewa dan kowa ce jam’iyyar siyasa. Shugabannin jam’iyyar APC sun shiga cikin rudani saboda sabbin mambobin da ke shigarta. Wasu daga cikinsu sun ce kodayake suna maraba da tsoffin ’yan PDP zuwa APC, ba za su samu mukamai ba a sabuwar gwamnatin.
Abin da ya dace shi ne jam’iyyun siyasar su yi amfani da wannan damar wajen gina kyakkyawan shugabanci ta hanyar fito da shiryr-shiryen da akidoji da za su dace da muradun masu zabe. Hakan ne zai taimaka wa masu kada kuri’a yin zabin da ya kamata madadin kalaman da ake rudin su da su.
A lokacin da jama’a suke da ikon bayyana ra’ayinsu a siyasance, ciki har da shiga jam’iyyun siyasa, bai kamata ’yan siyasa su sauya sheka ba domin kawai jam’iyyarsu ta fadi zabe. Makomar jam’iyyar PDP ta fuskar kara gina kanta da kara koma wa madafan iko a nan gaba ba abu ne da ba zai iya yiwuwa ba. Sai dai mambobin jam’iyyu masu rauni ba sa kawo ci gaban dimukradiyya.
Shugaban Jam’iyyar APC Cif John Odigie-Oyegun ya yi daidai lokacin da ya ce irin wannan tururuwar sauya shekar ba ta da kyau ga dimukradiyyar kasar nan. kasar nan na bukatar jam’iyyar adawa mai karfi domin cin moriyar zabukan da suka gabata.