Tururuwar ’yan gudun hijira daga Najeriya na karuwa a Kamaru

An samu karuwar ‘yan gudun hijira daga Najeriya zuwa kasar Kamaru a sakamakon rashin kwanciyar hankalin da jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa da ke makwabtaka da kasar Kamaru ke fama da shi.A yanzu haka dai wadansu ‘yan gudun hijira daga Najeriya da suke tsugune a wadansu garuruwa na arewacin Kamaru kamar su Fotokol […]

Tururuwar ’yan gudun hijira daga Najeriya na karuwa a Kamaru

n Mata da qananan yara ’yan Najeriya da ke gudun hijira a KamaruAn samu karuwar ‘yan gudun hijira daga Najeriya zuwa kasar Kamaru a sakamakon rashin kwanciyar hankalin da jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa da ke makwabtaka da kasar Kamaru ke fama da shi.
A yanzu haka dai wadansu ‘yan gudun hijira daga Najeriya da suke tsugune a wadansu garuruwa na arewacin Kamaru kamar su Fotokol da Amchide da kuma wadansu sassa daban da wakilinmu ya zanta da wadansu daga cikinsu sun nuna cewa suna rayuwa a cikin wani mawuyacin hali, duk da cewa hukumomi da wadansu ‘yan uwa a Kamaru sun karbi bakuncinsu, Hakan ya sanya ba su rasa samun abinci da kuma ruwan sha ba.
 Sai dai babbar matsala ita ce ta rashin samun labarin halin da wadansu ‘yan uwansu da suka bari a baya suke ciki, ganin cewa tun lokacin da aka kakaba wa wadansu jihohin Najeriya dokar ta-baci irin su Borno, Yobe da Adamawa aka katse layukan sadarwa.
Wata matsala kuma ita ce ta rashin tafiyar da harkokin kasuwanci saboda akasarinsu babu wata sana’a da suke yi. Kuma ga tsadar da dakunan haya suke yi, har idan mutum ya samu.Sa’annan kuma dada karuwa adadinsu yake yi. Wadansu na cewa yawansu ya kai sama da 4,000, ta garin Amchide mai makwabtaka da Banki na Jihar Borno.
Har ila yau kuma wata matsalar da wadannan mutane masu kaurar dole daga matsuguninsu zuwa wadansu wurare daban shi ne na samun karbuwa a wurin gwamnatin da suka bakunta. Saboda samun matsayin dan gudun hijira na farawa ne da yin rajista da kuma mallakar katin da zai tabbatar da matsayin da suke ciki.
A halin yanzu dai sama da ‘yan gudun hijira dubu dari daya ne suke zaune a kasar  Kamaru, akasarinsu kuma sun fito ne daga Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika. Duk da cewa kuma hukumar da take kula da su ta nuna cewa tana iyakar kokarinta na ganin cewa ta biya musu wadansu bukatunsu na yau da kullum, amma ‘yan gudun hijiran kokawa da halin rayuwar da suke ciki suka yi.
Wasu ‘yan gudun hijira sun bayyana wa wakilinmu irin halin da suke ciki, inda wata mata mai suna Martine ta ce, tun shekarar  2008 ta shigo kasar Kamaru kuma har yanzu ba ta samu wani wanda zai taimaka mata ta ciyar da yaranta uku ba.
Ita kuwa Marie Chantale cewa ta yi, ‘’rayuwa fa ba ta da sauki ga wanda ya bar kasarsa ya shiga wata kasa daban. Duk da cewa kashi 70 na daukacin bukatunmu Hukumar ‘yan gudun Hijira ta dauki nauyi, dole ne kuma mu ma mu yi kokari mu nemi na kanmu. Akwai wadanda suke yin katari, wadansu kuma suna kasawa.’’’
 Shi kuma Pierre bayani ya yi kamar haka, “mun samu karbuwa sosai a kasar Kamaru, amma sai dai rayuwa ba ta zuwa mana da sauki, musamman ma idan muka bukaci samun abin yi. Domin a nan Kamaru ma akwai tarin ‘yan kasa da suke zaman jiran tsammani.”
A bara can mafi yawan ‘yan gudun hijira na kasar Chadi sun koma gidajensu a kasarsu bisa ga ra’ayin kansu tare da taimkon gwamnatin Kamaru da ta kasarsu da kuma Hukumar da take kula da su,