Tushen zunubi da hanyar ceto (1)
Muna yi wa Ubangiji Allah godiya da Ya ba mu wannan zarafi domin mu yi bincike cikin maganarSa. A wannan mako za mu yi bincike ne a kan tushen zunubi da hanyar ceto. Bari mu fara da karatu a cikin Littafin Farawa 1:26-27: “Allah kuma Ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarMu da kamanninMu, […]
Muna yi wa Ubangiji Allah godiya da Ya ba mu wannan zarafi domin mu yi bincike cikin maganarSa. A wannan mako za mu yi bincike ne a kan tushen zunubi da hanyar ceto.
Bari mu fara da karatu a cikin Littafin Farawa 1:26-27: “Allah kuma Ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarMu da kamanninMu, su mallaki kifayen da suke cikin teku da tsuntsayen sararin sama da dabbobi da dukkan duniya da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa kasa.” Haka nan fa, Allah Ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah Ya halicci mutum, namiji da mace ya halicce su.”
Idan muka yi bincike cikin Littafin Farawa za mu ga yadda Ubangiji Allah Ya halicci mutum (Adamu) daga turbaya (kasa) Ya kuma hura masa rai.
Sa’an nan Ubangiji Allah Ya ce, “Bai kyautu mutumin ya zauna shi kadai ba, zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.” Haka nan fa, daga cikin kasar, Ubangiji Ya siffanta kowace dabba ta cikin saura da kowane tsuntu na sararin sama, Ya kawo su wurin mutumin, Ya ga yadda zai kiraye su, duk abin da mutumin ya kirayi mai ran kuwa, sunansa ke nan. Mutumin ya bai wa dabbobi duka suna da tsuntsayen sararin sama da kowace dabba da take cikin saura, amma ba a samu mataimaki wanda ya dace da mutumin ba.
Sai Ubangiji Allah Ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin. Lokacin da yake barci Ubangiji Allah Ya cire daya daga cikin hakarkarinsa Ya cike wurin da nama, hakarkarin nan kuwa da Ubangiji Allah Ya cire daga mutumin Ya yi mace da shi, Ya kuwa kawo ta ga mutumin. Sai mutumin ya ce, “Yanzu dai wannan kashi ne daga kasusuwana, nama ne kuwa daga namana, za a kira ta mace, don daga cikin mutum aka ciro ta.” (Farawa 2 18 – 24).
Bari mu ga wani abu mai muhimmancin gaske a nan, Ubangiji Ya halicci namiji da mace don su zauna tare, (zaman aure), bai halicci namiji da namiji ko kuma mace da mace su yi zaman aure ba, kamar yadda muke gani a zamaninmu na yanzu ba, sai mu lura.
Kada mu yi nesa da abin da muke nazari a kai. Da Ubangiji Allah Ya halicci duniya da duk abin da ke cikinta, Ya nufi mutum da ya ci moriyarta ya kuma bauta maSa amma sai mutum ya ba wa Shaidan zarafi ta wurin rashin biyyaya ga umarnin Ubangiji da Ya ce masa ya mallaki komai cikin gonar Adin amma kada ya ci daga ’ya’yan itacen da suke tsakiyar gonar. Kamar yadda za mu gani a Littafin Farawa 3: 2-5: “Sai matar ta ce wa macijin, “Ma iya ci daga cikin itatuwan gonar, amma Allah Ya ce, ‘Ba za ku ci daga cikin ’ya’yan itacen da yake tsakiyar gonar ba, ba za ku taba su ba, don kada ku mutu.’ Amma macijin ya ce wa matar, “Hakika ba za ku mutu ba. Gama Allah Ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su bude, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.”
Ubangiji Allah ne Ya halicce mu duka, Ya kuma shirya mana hanyoyin da za mu tafiyar da rayuwarmu a hanyar da ta dace. Amma Shaidan na gaba da wannan, shi ya sa za ka ga yakan fito ta hanyoyi daban-daban domin ya ga ya ci nasara a kanmu.
Akwai abubuwan da nake so mu lura da su a cikin karatunmu; na farko, Shaidan ya jarabci Hauwa’u, san’anan Adamu da Hauwa’u suka karya umarnin Allah ta wurin cin ’ya’yan itacen da Ubangiji Ya gargade su da kada su ci. Na uku, sun yi zunubi ne don suna neman girma, Shaidan ya ce wa matar; “…Hakika ba za ku mutu ba, gama Allah Ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su bude, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.”
Shaidan na da hanyoyi da dama da yake amfani da su na rinjayar mutane su bar tafarkin Ubangiji, yakan rudi mutum da karya. Yahaya 8:44 …”Shi da ma tun farko mai kisan kai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa’ar da yake karya, cinikinsa yake yi, don shi makaryaci ne, uban karairayi kuma. Laifin Adamu da Hauwa’u suka yi wa Ubangiji ta wurin rashin bin umarninSa ya kawo wahala da hallaka ga dukan duniya.
Shaidan na da hanyar rudin mutane da dama har wa yau ta hanyoyi daban-daban; yakan sa mutane sha’awar kayan duniya fiye da Mahaliccinsu, yakan cika zukatan mutane da mugunta, son kai da makamantansu.
Abin tambaya a nan shi ne, ta yaya mutun kan fada cikin wannan tarkon zunubi?
Mutum yakan iya fadawa cikin wannan tarko ta wurin kwadayin kayan duniya, neman matsayi, tsawon kwana, kamar yadda muka karanta da farko cikin Littafin Farawa 3:1. “Macijin (Shaidan) ya ce wa matar, “Ko Allah Ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itace da yake a gonar ba?’ Shaidan yakan zo ne ta hanyoyin da ba za ka zata zai kai mutum ga hallaka ba, zai rinjaye ka da kalamai ko abubuwa masu dadi, abin lura a nan shi ne, idan muka ga cewa wadannan abubuwan ba sa kan tafarkin Ubangiji, sai mu guje su. Mu kuma zama masu yin addu’a a kullum don Ubangiji Allah Ya kubutar da mu daga hanyoyin Iblis.