Tushen zunubi da hanyar ceto (2)
Barkanmu da sabuwar shekara. Bari Ubangiji Ya sa mana albarka, Ya kiyaye mu, Ya sa fuskarSa ta haskaka mu, Ya yi mana alheri, Ubangiji Ya dube mu da idon rahama, Ya ba mu salama a wannan sabuwar shekara mai albarka, amin. A wannan mako da yardar Ubangiji za mu ci gaba ne da nazarinmu a […]
Barkanmu da sabuwar shekara.
Bari Ubangiji Ya sa mana albarka, Ya kiyaye mu, Ya sa fuskarSa ta haskaka mu, Ya yi mana alheri, Ubangiji Ya dube mu da idon rahama, Ya ba mu salama a wannan sabuwar shekara mai albarka, amin.
A wannan mako da yardar Ubangiji za mu ci gaba ne da nazarinmu a kan tushen zunubi da hanyar ceto.
Makon jiya mun ga wasu hanyoyin da Iblis yakan rinjayi mutum don ya saba wa Ubangiji Allah ta wurin karya umarninSa. Hanyoyin nan kuwa har wa yau mutane da dama na fadawa cikinsu.
Adamu da Hauwa’u sun saba wa Ubangiji ta wurin karya umarninSa da Ya ce kada su ci daga ’ya’yan itacen da ke tsakiyar gonar, ta dalilin haka kuwa Ubangiji Ya ba su horo. Da farko sun karya dokar Ubangiji, na biyu, laifin da suka yi ya kawo mutuwa (mutuwa ta har abada), na uku, Ubangiji Ya ba su horo. Farawa 3:16-17, “Ga matar kuwa Ya ce, “Zan tsananta navudarki ainun da azaba za ki haifi ’ya’ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.” Ga Adamu kuwa Ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga ’ya’yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tunda ka aikata wannan za a la’antar da vasa saboda kai da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.”
Ta yaya suka yi zunubi har ya kai ga irin wannan faduwa?
Na farko, tunane zuciyar mutum: Matasa da dama sun shiga wata irin mummunar rayuwa domin kwadayin kayan duniya. Haka nan kuma wadansu mata sukan shiga halin karuwanci ko lalata da makamantansu, donmin neman kayan duniya. 1 Timoti 6:9-10 “Masu dokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fada a cikin tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin wadanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. Ai, son kudi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kudi kuwa wadansu mutane, har sun baude wa ban-gaskiya, sun jawo wa kansu bavin ciki iri-iri masu sukar rai. Mutane da dama na aikata miyagun halaye cikin zamanin da muke a yau, shin ta yaya mutum ke fadawa cikin irin wannan hali? Ta wurin tunani da kuma bai wa Shaidan dama ya shuka nasa iri cikin tunaninmu garin neman mafita cikin wani yanayin da mutum ya samu kansa a ciki ko kuma kwadayi da sha’awar kayan duniya.
(Karin Magana 4:23). «Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja ». Kamar yadda Hauwa’u ta yi, ta ji abin da Ibilis ya fada ta kuma aikata. (Far.3:6) : «Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, ’ya’yansa kuma kyawawa, abin sha’awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga ’ya’yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta wasu, shi kuma ya ci. Sai dukkansu biyu idanunsu suka bude, sa’an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen baure suka dindinka suka yi wa kansu sutura.»
Ubangiji Ya ba mu dama da iko bisa tunaninmu bai kuma bar mu haka ba, Ya nuna mana hanyar da za mu bi da shi. Idan muka duba cikin Littafin Yakubu 1:12-15 : «Albarka ta tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya samu kambin rai, wanda Ubangiji Ya yi wa masu vaunarSa alvawari. Duk wanda ake jarabta, kada ya ce Allah ne Yake jarabtarsa, gama ba ya yiwuwa a jarabci Allah da mugunta, shi kanSa kuwa ba Ya jarabtar kowa. Amma kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya rude shi, ya kuma yaudare shi. Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.”
Yesu ya ce a Littafin Matiyu 5:27-28: “Kun dai ji an fada, ‘Kada ka yi zina.’ Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha’awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita.” Idan muka koma aya ta 21-22, “Kun dai ji an fada wa mutanen da, ‘Kada ka yi kisan kai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’ 22 Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da dan uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da dan uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ Havvinsa shiga Gidan Wuta.”
Domin haka, sai mu kare tunaninmu kafin Shaidan ya cusa mana nasa ra’ayin har mu bar tafarkin Ubangiji.
Tafarkin Ubangiji hanya ce mai adalci, mai aminci, mai gaskiya kuma. Maimaitawar Shari’a: 32:3,4: “Gama zan yi shelar sunan Ubangiji, In yabi girman Allahnmu! “Shi dutse ne, aikinSa kuma cikakke ne, Gama dukan hanyoyinSa masu adalci ne. Allah Mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare Shi, Shi Mai adalci ne, Nagari ne kuma. »
A wannan sabuwar shekara bari mu lura da yadda muke tafiyar da rayuwarmu, mu nemi fuskar Ubangiji cikin komai, Shi kuwa zai jagorance mu kan hanyarSa.
Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah Ya ba rmu cikin rayyayyu.
Bari Ubangiji Allah Ya albarkace mu, amin.