Tutar sojan Japan ta haifar da rikici tsakanin Japan da Koriya ta Kudu
kyallaye da tutocin soja da aka daga a wajen wasann kwallon kafa, sun haifar da yamutsi a tsakanin manyan jami’an gwamnatin kasashen Japan da Koriya ta Kudu. Don haka Hukumar Wasan kwallon kafa ta Koriya (KFA) ta bayar da sanarwa a Larabar da ta gabata cewa, magoya bayan Japan su suka harzuka magoya bayan Koriya […]
kyallaye da tutocin soja da aka daga a wajen wasann kwallon kafa, sun haifar da yamutsi a tsakanin manyan jami’an gwamnatin kasashen Japan da Koriya ta Kudu. Don haka Hukumar Wasan kwallon kafa ta Koriya (KFA) ta bayar da sanarwa a Larabar da ta gabata cewa, magoya bayan Japan su suka harzuka magoya bayan Koriya ta kudu, a lokacin da suka daga tutar sojojin Japan “mai alamar rana,” a wajen gasar kwallon kafa na cin kofin Gabashin Asiya, da ake yi a birnin Seoul.
Magoya bayan da ake wasan a gidansu, wato ’yan Koriya ta Kudu, su ma sun koma sun rubuto kyallensu da tutarsu mai dauke da bayanan da ke cewa: “Babu makoma ga mutanen da suka manta da tarihinsu,” wato al’amarin da ke nuni da mamayar da Japan ta kai wa kasarsu a tsakanin shekarun 1910 zuwa 1945.
Mafi yawan al’ummar Koriya ta Kudu, na da tabbacin cewa Japan ta kasa neman afuwar cin mutuncin da ta yi wa al’umma a lokacin mulkin mallakar da ta yi wa kasar, al’amarin da har yanzu ke haifar da rikici a tsakanin kasashen biyu.