Tuwo miyar kuka
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri. A yau na kawo muku yadda ake tuwo miyar kuka. Lallai wannan irin girki ne wadda yara da dama basu cika so ba. Kasancewar yadda wadansu mata ke girkawa. Ko kun san cewa wannan miyar ba ta karamin gida bace idan har an san yadda za a sarrafa […]
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri. A yau na kawo muku yadda ake tuwo miyar kuka. Lallai wannan irin girki ne wadda yara da dama basu cika so ba. Kasancewar yadda wadansu mata ke girkawa. Ko kun san cewa wannan miyar ba ta karamin gida bace idan har an san yadda za a sarrafa ta?
Wannan miya ce ba na hana yaro kuka ba, har ma da manya. Domin babu abin da ya kai ta sauki wajen hada ta musamman idan aka hada da tuwon masara ko dawa. A ci dadi lafiya.
Abubuwan da za a bukata
• Kuka
• Tafarnuwa
• Banddar kifi
• Kaza/nama
• Citta
• Attarugu
• Albasa
• Magi
• Kori
• Man shanu
• Daddawa
Hadi
Da farko Uwar gida za ta wanke kazarta ko nama yadda ya kamata sannan ta daura a wuta. Ta yayyanka albasa da tafarnuwa da dan gishiri kadan sosai, har hadin ya tafasa. Sannan ta dauko kifi banda kamar daya ta wanke da ruwan zafi sannan ta zuba. Ta jajjaga attarugu hade da tafarnuwa da daddawa sai sunyi laushi sannan ta zuba. Ta samu garin citta kadan ta zuba da magi da kuma kori.
Idan an fara jin kamshin kifi ya bayyana, alama ce cewa kifin ya nuna sannan a tsame kazar ko namar a ajiye a gefe sannan a debo garin kuka a rika kadawa kadan-kadan ta yadda ba za ta yi gudaji ba. Sannan ta rage wuta ya dan sake tafasa kadan. Idan tana bukatar sanya tokar miya, sai ta zuba kadan ta sake gaurayawa sannan ta sauke.
A tuka tuwon dawa ko na masara ko kuma na shinkafa sannan aci da man shanu.