Tuwo ya yi ajalin mutum 9 ’yan gida daya a Zamfara
Likitoci sun tabbatar akwai guba a tuwon da suka ci.
Wani mummunan lamari ya faru a kauyen Jangebe da ke cikin Karamar Hukumar Gusau a Jihar Zamfara yayin da wasu ’yan gida daya tara suka mutu bayan sun ci abinci mai dauke da guba.
Kawun yaran da suka rasu mai suna Abdullahi Bello, ya shaida wa Aminiya cewar, yaran sun rasa rayukansu ne bayan ’yar uwarsu ta kawo musu ziyara kuma ta girka musu abinci.
- PDP na da yakinin samun nasara a zaben 2023 —Secondus
- Kasashen da Nnamdi Kanu ya je kafin a kama shi
“Lokacin da ta zo, sai ta debo hatsi sannan ta tafi da shi aka niko. Kuma bayan haka wani bera ya mutu a cikin garin dawar tun kafin a tuka tuwon.
“Kuma ba wanda ya lura cewar garin tuwon ya gurbata, don haka bayan ta kammala yara suka ci tuwon, sai yaro daya daga cikin wadanda suka ci tuwon ya mutu.
“Daga nan muka tafi da sauran yaran zuwa asibiti a Gusau, nan ma biyu daga cikinsu suka sake mutuwa a asibitin.
“Mun dauki gawarsu don mika su zuwa makwancin karshe, muna makabarta ake sake sanar da mu wasu sun sake mutuwa.
“Yara bakwai ciki da ’yar uwarsu da ta yi girkin da mahaifiyarsu baki daya sun rasu,” a cewar Abdullahi.
Iyayen yaran ba sa nan lokacin da mummunan lamarin ya faru, don haka sun shiga cikin wani mawuyacin hali bayan samun labarin faruwar lamarin.
Tuni gidan ya zama tamkar kufai sakamakon yadda mutuwar ta yi wa yaran gidan yankan kauna.
Wakilinmu da ya ziyarci Asibitin Kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau, ya samu yaro daya rai a hannun Allah likitoci na ta kokarin ceto rayuwarsa.
Jami’in hulda da jama’a na asibitin, Awwal Usman RuwanDorawa ya shaida wa Aminiya cewar “Likitocin sun tabbatar da gubar da suka ci a abinci ne ta yi ajalinsu”.
Ya ce likitocin sun yi iya kokarinsu don ceton rayukansu, amma abun ya faskara saboda rashin kawo su asibitin a kan lokaci.