UAE ta dakatar da ba ’yan Najeriya bizar zuwa Dubai

Haramcin bizar zuwa Dubai ya shafi kowa a Najeriya

UAE ta dakatar da ba ’yan Najeriya bizar zuwa Dubai

Hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun dakatar da bayar da biza ga ’yan Najeriya masu son zuwa Dubai.

Sanarwar hakan na kunshe ne a wata takarda da gwamnatin kasar ta aiko wa hukumomi Najeriya da kuma masu shirya tafiye-tafiye a ranar Juma’a.

A cewar Tribune, takardar ta fito karara ta bayyana cewa “ duk wata bukatar izinin zuwa Dubai ba za a karbe ta ba”.

Sananan ta kara da cewa, “Wannan kin bayar da izinin ya shafi kowa a Najeriya.”

Lafazin takardar na nufin hatta jami’an hukumomi da kuma gwamnati, ba za a ba su bizar ba, har sai nan da wani lokaci.

Ga wadanda suka mika tarkardun bukatarsu, suka kuma biya, ba za a mayar musu da kudadensu ba, a cewar rohoton.

Wannan hanin shi ne mataki da kasar UAE ta dauka na baya-bayan nan tsakaninta da Najeriya.

Kasar ba ta kuma bayar da dalilin daukar wannan mataki kan ’yan Najeriyar ba.