UAE ta kusa fara bai wa ’yan Najeriya biza — Keyamo

Keyamo ya ce yana da masaniyar lokacin da gwamnatin UAE za ta ɗage dokar.

UAE ta kusa fara bai wa ’yan Najeriya biza — Keyamo

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), za ta ɗage dokar haramcin bai wa ’yan Najeriya biza domin shiga ƙasar.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne, ya bayyana hakan a wata hira ta mintuna 44 da ya yi da babban mai taimaki na musamman ga Shugaba Bola Tinubu, Otega Ogra.

An wallafa hirar ne a shafin YouTube na fadar shugaban ƙasa.

Keyamo, ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu da shugaban UAE Mohamed bin Zayed Al Nahyan sun cimma yarjejeniya yayin ziyarar da Tinubu ya kai Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Satumban 2023.

Duk da cewar akwai matakai da ya kamata a cimma, amma ana sa ran sanarwar daga gwamnatin UAE nan ba da jimawa ba.

“Bayan wannan muhimmin taro, shugaba Tinubu ya sauƙaƙa mana al’amura. Mun bi sahun lamarin a matsayinmu na ministocinsa kuma muka warware komai.

“Yanzu, sai dai mu jira gwamnatin UAE ta sanar da hakan,”in ji Keyamo.

Keyamo ya kuma bayyana cewa ya san lokacin da za a ɗage dokar hana tafiye-tafiye, amma ya ce wuƙa da nama na hannun gwamnatin UAE wajen sanar da hakan a hukumance.

Ɗage haramcin zai sauƙaƙa wa ’yan Najeriya da ke tafiye-tafiye zuwa UAE, kuma zai inganta dangantaka da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.