Uba Da Ɗa Sun Hallaka Matar Aure A Edo

Wani uba da ɗansa sun raba wata mata da duniya sanadiyyar wata hatsaniya da ta shiga tsakaninsu a Jihar Edo. Mista Philip Ayo da dansa sun yi ajalin  matar auren mai suna Misis Nata Igbinovia a daren  Asabar ne. Matar da ke zaune unguwar Okpagha da ke karamar hukumar Uhunmwode ta rasa ranta ne sakamakon […]

Uba Da Ɗa Sun Hallaka Matar Aure A Edo

’Yan sanda. (Hoto: NAN)

Wani uba da ɗansa sun raba wata mata da duniya sanadiyyar wata hatsaniya da ta shiga tsakaninsu a Jihar Edo.

Mista Philip Ayo da dansa sun yi ajalin  matar auren mai suna Misis Nata Igbinovia a daren  Asabar ne.

Matar da ke zaune unguwar Okpagha da ke karamar hukumar Uhunmwode ta rasa ranta ne sakamakon rabon fada tsakanin ɗan uwanta da makwabtantanta,

A cikin haka ne sai wanɗanda ake zargin suka mayar da faɗan kanta kuma suka yi ajalinta.

Yar matar da aka hallaka ta bayyana cewa, waɗanda ake zargin sun caccaka mata wuƙa a ƙirji, kuma sun sara mata gatari a gadon bayanta, lamarin da ya yi sanadiyyar barinta duniya.

Daga nan ne aka samu wani bawan Allah ya garzaya da mahaifiyar tata asibiti, inda aka tabbatar musu da cewa ta cika.

Kakakin ’yan sandan a Jihar Edo ya tabbatar mana da faruwa lamarin da kuma kama waɗanda ake zargin.