Uba da ’ya sun mutu a rijiya a Kano

Mutumin ya rasu tare da ‘yarsa a cikin rijiyar.

Uba da ’ya sun mutu a rijiya a Kano

Wani mutum da ’yarsa sun rasu bayan sun faɗa rijiya a garin ’Yancibi da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, inda mutumin mai suna Abubakar Abdullahi mai shekaru 45, ya shiga rijiyar domin ceto ’yarsa, Fiddausi, mai shekaru 15 bayan ta faɗa ciki.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara na Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdyllahi, ya ce sun yi yunƙurin ceto mutanen biyu, amma saboda duhun rijiyar da kuma rashin kyakkyawan yanayi suka gaza yin hakan.

“A ranar Laraba ne da safe muka tashi tawaga domin ceto su. Mun ciro su da ƙyar bayan sun fita hayyacinsu. Daga bisani suka rasu.” In ji shi.

Daga nan ne ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da al’ummar garin, tare da gargaɗin su kan shiga rijiya ba tare da kayan aikin da suka dace ba.