Uba Sani ya mayar wa iyalan Abacha filayen da El-Rufai ya ƙwace musu
Lauyan iyalan Abacha, Reuben Atabo, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya mayar wa iyalan Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Sani Abacha, filayensu guda biyu da tsohon jihar, Nasir El-Rufai ya ƙwace a lokacin mulkinsa.
Lauyan iyalan Abacha, Reuben Atabo, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
- SON ta gargadi masana’antu kan bi ka’idoji wajen sarrafa kayayyaki
- Gwamnatin Jigawa ta bankado ma’aikatan bogi 6,348
A cewar sanarwar da Babban Daraktan Ma’aikatar Kula da Filaye ta Jihar Kaduna, Mustapha Haruna ya fitar, Gwamna Uba Sani ya aike wa iyalan Abacha wasiƙa.
A wasiƙar, an tabbatar da mayar musu da filayen sannan an buƙaci su biya harajin da aka saba karɓa sakamakon mallakar filayen.
Tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya ƙwace filayen ne a ranar 28 ga watan Afrilun 2022.
Bayan ƙwace filayen, ya sanar da matakin nasa a cikin jaridu tare da soke
Sai dai matakin na El-Rufai ya haifar da cece-kuce, inda wasu ke ganin tsohon gwamnan bai kyauta ba.