Uba Sani ya rage karin kudin makarantu da El-Rufai ya yi a Kaduna
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya rage kudin manyan makarantu da tsohuwar gwamnatin jihar ta kara. Sanata Sani ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa ranar Litinin a shafinsa na Facebook, yana mai cewa rage kudin makarantun na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma ke koken yadda tsadar kudin makarantun ya […]
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya rage kudin manyan makarantu da tsohuwar gwamnatin jihar ta kara.
Sanata Sani ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa ranar Litinin a shafinsa na Facebook, yana mai cewa rage kudin makarantun na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma ke koken yadda tsadar kudin makarantun ya jefe su cikin zulumi.
- Cancanta muka duba wajen zaɓo ministoci — Tinubu
- ’Yan ta’adda sama da 100 sun mutu a gumurzu tsakanin Boko Haram da ISWAP
A cewarsa, rage kudin makarantun ya yi daidai kudirin gwamnatinsa na samar da tallafi domin rage kuncin rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu, musamman bayan cire tallafin man fetur da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.
“Inganta walwala da jin dadin alummar shi ne abin da muka bai wa fifiko.
“Gwamnatinmu za ta ci gaba daukar matakai da aiwatar da duk mai yiwuwa domin saukaka neman ingataccen ilimi a Jihar Kaduna tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu na gaba da sakandire.
Haka kuma, za mu ci gaba da bunkasa harkokin ilimi ta hanyar inganta walwala da jin dadin malamai.”
Yadda alkaluman rage kudin ya kaya:
Jami’ar Kaduna
Kudin Makaranta: N150,000
Ragi: Kashi 30
Sabon Kudin: N105,000
Makarantar Kimiyya ta Nuhu Bamalli:
Kudin Makaranta: N100,000
Ragi: Kashi 50
Sabon Kudin Makaranta: N50,000
Kwalejin Ilimi Gidan Waya
Kudin Makaranta: N75,000
Ragi: Kashi 50
Sabon Kudin Makaranta: N37,500
Kwalejin Kimiya da Fasahar Lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi
Kwasa-Kwasan Babbar Difloma (HND)
Kudin Makaranta: N100,000
Ragi: Kashi 30
Sabon Kudin Makaranta: 70,000
Kwasa-Kwasan Karamar Difloma (ND)
Kudin Makaranta: N75,000
Ragi: 30
Sabon Kudin Makaranta: N52,000
Kwalejin Koyon Aikin Jinya
Kudin Makaranta: N100,000
Ragi: Kashi 30
Sabon Kudin Makaranta: N70,000.