Uba ya ba ’yar cikinsa kwaya, ya yi mata fyade a Ogun

Wani mutum da ake zargin ya ba ’yarsa kwaya, sannan ya yi mata fyade ya shiga hannun ’yan sanda

Uba ya ba ’yar cikinsa kwaya, ya yi mata fyade a Ogun

Wani mutum da ake zargin ya ba ’yarsa kwaya, sannan ya yi mata fyade ya shiga hannun ’yan sanda a jihar Ogun.

Mutumin, mai shekara hamsin ya shiga hannun jami’an kungiyar tsaro ta Jihar Ogun, mai suna So-Safe da ke Karamar Hukumar Ifo ta Jihar Ogun a ranar Alhamis.

Kakakin kungiyar tsaron, Moruf Yusuf ya shaida wa ’yan jarida a garin Abeokuta a ranar Juma’a, cewa, “Rundunar mu ta samu wani kira na gaggawa a inda ake fada mana cewa mutumin ya yi wa ’yar cikinsa fyade,”.

Ya ce da kyar kwamandan yankin ya kwato wanda ake zargi daga fusatattun jama’ar wurin da ke kokarin kashe shi, bayan jin abin da ya aikata.

‘Yar wanda ake zargi, wacce aka boye sunanta, ta zargi babanta da cewa, wannan ba shi ne karon farkon ba da yake yi mata haka ba.

Tuni dai kungiyar tsaron ta mika wanda ake zargi hannun ’yan sanda.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota