Uba ya bukaci sadakin dabino da kofin gahawa don aurar da ’ya’yansa a Hadaddiyar Daular Larabawa

Wani uba ya bukaci sadakin dabino da kofin shayin gahawa daga duk mai son auren daya daga cikin ’ya’yansa shida, a masarautar Al Ain ta Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan al’amari ya saba wa yadda aka sha jin labarin sadaki mai tsada, inda har amfani ake yi da zinari a matsayin sadaki.An ruwaito cewa, wannan mahaifin […]

Uba ya bukaci sadakin dabino da kofin gahawa don aurar da ’ya’yansa a Hadaddiyar Daular Larabawa
Uba ya bukaci sadakin dabino da kofin gahawa don aurar da ’ya’yansa a Hadaddiyar Daular Larabawa

Wani uba ya bukaci sadakin dabino da kofin shayin gahawa daga duk mai son auren daya daga cikin ’ya’yansa shida, a masarautar Al Ain ta Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan al’amari ya saba wa yadda aka sha jin labarin sadaki mai tsada, inda har amfani ake yi da zinari a matsayin sadaki.
An ruwaito cewa, wannan mahaifin ’ya’ya mata shida ya fahimci cewa, mafi yawan mutanen Hadaddiyar Daular Larabawa na yin aure da kyar ko ma su gaza saboda tsadar sadaki; a wani yanayin ma har harkar auren ta jefa su cikin matsanancin bashi. Wasu kuwa tsadar auren kasar kan sanya su su auri bakin da suka shigo daga wta kasa.
Jaridar Khaleej Times ta taba ruywaito cewa, aure tsakanin baki da maza ’yan asalin Hadaddiyar Daular Larabawa ya fara habaka tun daga shekarar 2012. Wannan ne dalilin da ya sanya ake da dimbin mata wadanda ba su yi aure ba.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano