Uba ya kashe dansa kan tutar jam’iyyar siyasa
Mahaifin ya harbi dan nasa mai shekaru 31 da bindiga saboda tutar jam’iyyar siyasa
Wani mahaifi ya harbe dansa har lahira saboda tutar jam’iyyar siyasa gabanin zaben kasar Pakistan da ke tafe.
Hukumomin ’yan sandan kasar sun ce mutumin da dan nasa sun samu sabani ne kan tutar jam’iyyar da za a sanya a jikin gidansu a kakar zaben.
Sun bayyana cewa dan, wanda kwanan nan ya dawo gida daga inda yake aiki a Qatar, ya sanya tutar Jam’iyyar PTI ta tsohon fira ministan Pakistan Imran Khan, a gidan nasu da ke yankin Peshawar da ke Lardain Khyber Pakhtunkhwa.
Amma sai mahaifin wanda kafin yanzu ya sanya tutar Jam’iyyar ANP a gidan, “ya haramta wa dan nasa sanya tutar PTI a gidan, amma duk da haka, dan ya ki sauke tutar ko daine goyon ban jam’iyyar.
- An kama shugaban karamar hukuma kan yunkurin kashe Shugaban Majalisar Benuwe
- ’Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun sace mutane 29 a Katsina
“Daga bisani lamarin ya yi zafi, inda cikin fushi mahaifin ya ciro karamar bindiga ya harbi dan dan nasa mai shekaru 31, sannan ya tsere daga gidan,” in ji wani jami’in dan sanda.
Jami’in ya bayyana cewa dan ya rasu ne a hanyar zuw asibiti kuma a halin yanzu an baza komar neman mahaifin.
A ranar 8 ga Fabrairun shekarar nan ta 2024 ne za a a gudanar da babben zaben kasar Pakistan mai cike da rikici, innda a lokuta da daman an kai hari kan masu takara a zaben.