Uba ya sa kyamarar sa-ido a kan ’yarsa

A cikin wani faifan bidiyo mai suna ‘Next Level Security’ an nuna matar ’yar Pakistan ana hira da ita a yayin da take rataye da na’urar kyamarar CCTV a kanta.

Uba ya sa kyamarar sa-ido a kan ’yarsa

Wani mahaifi a kasar Pakistan da ke son kare ’yarsa daga barazanar cin zarafi ya ya sa mata kyamarar CCTV a kanta don sa mata ido sosai.

Babu wani abu da iyaye na gari ba za su yi ba don tabbatar da kula da lafiyar ’ya’yansu.

Misali, labarin wani ɗan kasar Pakistan kwanan nan ya yaɗu sosai a shafin sada zumunta na X (Twitter) saboda saka kyamarar sa ido a kan ’yarsa da ya yi don ya kula da harkokinta a tsawon rana kuma ya tabbatar da cewa tana cikin koshin lafiya.

A cikin wani faifan bidiyo mai suna ‘Next Level Security’ an nuna matar ’yar Pakistan ana hira da ita a yayin da take rataye da na’urar kyamarar CCTV a kanta.

Da aka tambaye ta game da hakan, ta ce ra’ayin mahaifinta ne, inda ta kara da cewa ba ta da wani abin cewa game da kyamarar kanta saboda ta san iyayenta sun damu da kulawa da lafiyarta.

Matar da a aka sakaya sunanta, ta ci gaba da cewa, tunanin saka na’urar da ake zaton na’urar ɗaukar hoto ce mai amfani da batir a lokacin da za ta fita, ya samo asali ne daga mutuwar wata budurwa a garin Karachi.

Mahaifinta, wanda ta kira da “mai ku;a da lafiyarta duk inda take,” da alama ya gaya mata cewa kyamarar sa-ido za ta taimaka masa ya kula da ita sosai, kuma ta yarda ta ɗaura kyamarar.

Duk da matakin da ake kira matakin tsaro, yarinyar ta yi ikirarin cewa barazanar cin zarafin mata a Karachi gaskiya ce, kuma iyayenta suna da cikakken dalilin damuwa.

Ba a dai bayyana yadda ake amfani da kyamarar sa ido ba da kuma yadda sakon zai iya kaiwa ga mahaifin matar, amma shafukan sada zumunta sun nuna cewa, kyamarar ba za ta yi amfani sosai ba, idan wani ya kai wa yarinyar hari ta baya. Haka kuma, watakila iyayenta suna dogara ga cewa ganin kyamarar tsaron zai tsoratar da duk wanda ke da mummunan nufi kan ’yarsu.

Tags