Uba ya sayar da dansa mai shekara 9 kan Naira 400,000

Ya ce matsin tattalin arziki ne ya sanya shi aikata hakan

Uba ya sayar da dansa mai shekara 9 kan Naira 400,000

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Akwa Ibom ta kama wani mahaifi, Gabriel Ekpiri, bisa zarginsa da sayar da dansa mai shekara tara a duniya a Karamar Hukumar Itu ta Jihar.

Kakakin rundunar a Jihar, Odiko MacDon, ne ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa ranar Laraba, inda ya ce jami’ansu masu kai daukin gaggawa ne suka kai samamen da ya kai ga kama shi.

Ya ce lokacin da jami’ansu suka titsiye shi, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin, inda ya zargi matsin tattalin arzikin da ake ciki da cewa shi ya jefa shi ya aikata hakan.

Sanarwar ta ce, “Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Akwa Ibom, Olatoye Durusinmi, ya yi Allah wadai da abin da wani mai suna Gabriel Ekpiri, na yankin Ekit Itam Akpan Obong da ke Karamar Hukumar Itu, ya aikata na sayar da dan cikinsa kan Naira 400,000.

“Kwamishinan ya lura cewa wannan aikin jahilci ne kuma ba za a lamunce shi ba. Sashen kai daukin gaggawa na rundunarmu ne ya kama shi, kuma ya amsa aikata laifin, inda ya zargi Shaidan da matsin tattalin arziki a kan haka,” in ji sanarwar.

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025