Uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyade

Ya kawo rahoton asibiti na karya bayan ya yi wa ’yarsa mai shekaru takwas fyade

Uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyade

Wani mai sayar da maganin gargajiya ya gurfana a gaban kotu bisa zarginsa da yi wa diyarsa mai shekaru takwas fyade.

An gurfanar da magidancin mai shekaru 35 a kan tuhume-tuhume guda na fyade, wanda rundunar ‘yan sandan ta ce ya saba wa sashe na 25 (a) na dokar cin zarafin jama’a ta jihar Ondo ta shekarar 2021.

Dan sanda mai shigar da kara, Sufeto Martins Olowofeso, ya shaida wa kotun cewa an kama wanda ake kara ne a ranar 18 ga watan Yuni, 2024 bayan rahoton da aka kai ga sashin yaki da garkuwa da mutane na ’yan sanda a Alagbaka, cewa ya yi wa ’yarsa fyade.

Daga bisani an tsare wanda ake tuhuma don ci gaba da bincike.

A cewar Mista Olowofeso, wanda ake zargin tare da matarsa ​​sun gudu daga gidansu bayan aikata laifin inda suka je Jihar Osun suka samo rahoton likita na karya, da ke nuna babu wani abu da ya samu yarinyar.

Ya kuma shaida wa kotun cewa jami’in bincike na ’yan sanda ya sake yin wani gwaji a Akure, wanda ya nuna cewa an zakke wa yarinyar, kuma ta kwashe kwanaki uku tana zubar da jini.

A cewar Olowofeso, wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake zargin sa da shi a lokacin da jami’in da ke binciken ya yi amsa tambayoyi.

Olowofeso ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali na Olokuta har zuwa lokacin da za ta samu da shawara daga sashen shigar da kara na gwamnati (DPP).

Lauyan wanda ake kara, G.O Omoedu, ya shaida wa kotun cewa an kai wa wanda yake karewa sammaci kurarren lokaci kuma zai bukaci lokaci domin ya mayar da martani kan batun shari’a.

Ya bukaci kotun da ta dage ci gaba da shari’ar don ba shi damar amsa bukatar ci gaba da sauraren karar.

Majistare B.A. Alipohul ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara a hannun ’yan sanda sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Yulin 2024.

 

Rabon Awaki bai dace da Gwamnan Kano ba — Jaafar Jaafar

An tsinci gawar magidanci a rijiya a Kano

’Yan fashi sun hallaka mutum 7 a harin Kasuwar Ngalda da ke Yobe

Gwamnati ta musanta bai wa kamfanin bogi kwangilar titin Kano zuwa Abuja