Uba ya yi wa ’ya’yansa uku fyade
An kama magidanci ya yi wa ’ya’yan cikinsa masu kananan shekaru fyade
An kama wani magidanci mai shekara 48 kan yi wa ’ya’yan cikinsa uku masu kanana shekaru fyade.
Shekarun ’ya’yan sun kama daga babbar mai shekara takwas, sai mai shekara uku da karamar mai shekara daya da rabi.
- Janar Farouk Yahaya ya zama Babban Hafsan Sojin Kasa
- Hatsarin jirgin Kebbi: An kara gano gawa 13
- EFCC ta kwace gidajen ma’aikacin Fadar Shugaban Kasa
Yayin gabatar da magidancin, Hukumar tsaro ta Sibil Difens a Jihar Anambra ta ce wasu kungiyoyin farar hula ne suka tsegunta mata cewa mutumin yana lalata da ’ya’yan cikinsa.
“Da muka samu rahoton sai muka kame shi… Daga bisani jami’an lafiyar hukumarmu sun tabbatar da cewa an yi lalata da kananan ’yan matan.
“Wanda ake zargin ya amsa aikata danyen aikin kuma nan da ba da jimawa ba idan muka kammala bincike za mu gurfanar da shi a gaban kuliya,” inji kwamandan hukumar na jihar, David Bille.