Uban goyon El-Rufa’i Malam Yahaya Hamza ya rasu

Uban goyon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, Malam Yahaya Hamza ya rasu. Marigayin wanda fitaccen masanin ilimi ne da ya kai matsayin Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ya rasu ne a ranar Talata a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya yana da shekara 80 kamar yadda kakakin Gwamna El-Rufa’i Samuel Aruwan ya […]

Uban goyon El-Rufa’i Malam Yahaya Hamza ya rasu
Uban goyon El-Rufa’i Malam Yahaya Hamza ya rasu

Uban goyon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, Malam Yahaya Hamza ya rasu. Marigayin wanda fitaccen masanin ilimi ne da ya kai matsayin Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ya rasu ne a ranar Talata a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya yana da shekara 80 kamar yadda kakakin Gwamna El-Rufa’i Samuel Aruwan ya fadi a wata sanarwa.
Fitaccen ma’aikacin gwamnati marigayi Malam Yahaya Hamza ya taba zama Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, kuma tsohon Shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC).
Gwamna El-Rufa’i ya ce zai “rashin hikima da shawarwari daga wannan babban mutum wanda ya zama uba gare ni kuma jagora tsayayye.”
Ya roki Allah Ya saka masa da Aljannar Firdausi tare da ba iylansa hakurin jure wannan babban rashi.
Malam Yahaya Hamza ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya da jikoki da tattaba kunne kuma an yi jana’izarsa a shekaranjiya Laraba a Kaduna.
Shugaban Majalisar Wakilai Barista Yakubu Dogara na cikin mutane na farko da suka aike da sakon ta’aziyya ga Gwamna El-Rufa’i dangane da rashin uban goyon nasa.
Ta’aziyyar wadda take kunshe a wata takarda dauke da sanya hannun kakakin shugaban Turaki Hassan da aka raba wa manema labarai a Abuja ta ruwaito Dogara yana addu’ar Allah Ya ba iyalan marigayin hakurin jure wannan babban rashi.
Ya ce Malam Yahaya Hamza ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen tarbiyya da renon El-Rufa’i kamar yadda Gwamna ya fadi a cikin littafin tarihinsa, “The Accidental Public Serbant.”
“Shugaban yana jimamin rasuwar Hamza ta zo ne a lokacin da El-Rufa’i yake bukatar shawarwari da jagorancinsa wajen tafoyar da mulkin Jihar Kaduna.”
Dogara ya kuma yaba gagarumar gudunmawa da marigayin ya bayar inda ya bayyana shi da fitaccen masani kuma kwararre da ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa ilimi a Najeriya.