Ubangiji Shi ne karfina (1)
A wannan makon za mu yi bincike ne a kan jarabawa daban-daban da muke fuskanta a cikin rayuwarmu ta yau da kulum. A takaice dai babu wani mai rai da zai ce bai taba fuskantar jarabawa a rayuwarsa ba. Jarabawar na zuwa mana ne ta hanyoyi daban-daban; takan iya zama ta bangaren rashin lafiya ko […]
A wannan makon za mu yi bincike ne a kan jarabawa daban-daban da muke fuskanta a cikin rayuwarmu ta yau da kulum. A takaice dai babu wani mai rai da zai ce bai taba fuskantar jarabawa a rayuwarsa ba. Jarabawar na zuwa mana ne ta hanyoyi daban-daban; takan iya zama ta bangaren rashin lafiya ko rashin dukiya ko a wurin aiki ko a tsakanin iyali da makamantansu. Abin tambaya a nan shi ne, jarabawa na zuwa ga wanda ya yi zunubi ne kadai? Bari mu ga amsarmu a cikin Littafi Mai tsarki.
Ayuba 1:1-31, 6 -12; Akwai wani mutum a ƙasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ƙin aikata kowace irin mugunta. Yana da ’ya’ya bakwai maza, uku mata. Yana da tumaki dubu bakwai da raƙuma dubu uku da shanu dubu daya da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki. 6-12 Sa’ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta yi, Shaiɗan ma ya zo tare da su. Sai Ubangiji Ya tambaye shi, Ya ce, “Kai fa me kake yi?”Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, a ko’ina a duniya.” Ubangiji Ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.” Shaiɗan ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maKa sujada? Ai, don Ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, Ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasar nan. Amma da a ce za Ka raba shi da dukkan abin hannunsa, to, da zai fito fili ya zage Ka ƙiri-ƙiri.” Ubangiji Ya ce da Shaiɗan, “To, shi ke nan, dukkan abin hannunsa yana cikin ikonka, amma shi kansa kada ka cuce shi.” Sai Shaiɗan ya tafi.
A nan mun ga cewa Ayuba mutum ne mai tsoron Allah, natsattse, mai kin kowace irin mugunta yana kuma da arziki mai yawa, amma me ya faru? A aya ta 6 zuwa 12 mun ga cewa Allah Ya ba wa Shaiɗan damar jarabtar Ayuba. Abin lura a nan shi ne, duk jarabawa daban-daban da muke fuskanta a cikin rayuwarmu, Allah na sane da su, kada kuma mu ga cewa ai Allah ba Ya kaunarmu, sam, sam. Allah ne Ya halicce mu, Shi Ya ba mu rai, Yana kuma da iko bisanmu. Sau da dama za ka ga mutane a cikin rashin sani idan abu ya faru da su misali a ce mutuwar uba, uwa ko da, ko kuma mu ce dukiyarsu ta kone ta wurin hadarin wuta, za ka ga suna kuka suna tambaya me ya sa Allah Ya bar abu haka ya faru da su? A ganinka abin da ya kamata su yi ko kuma su fadi ke nan a irin wannan lokaci? Babu shakka irin wannan yanayi na da matukar zafi a zuci, amma Ubangiji Allah Ya ce mana a Littafin 1 Korantiyawa 10:13 “Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan Adam ba. Allah Mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin karfinku ba, amma a game da gwajin sai Ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.” Tabbacin yana da sanin duk matsalolin da muke ciki, Ya kuma ba mu abin da zai taimake mu a irin wannan lokuta, wato maganarSa da saninSa. Sanin Ubangiji kadai zai sa mu gane kowane irin yanayi da muka fada ciki. Ishaya 41:13. “Ni ne Ubangiji Allahnku, Na karfafa ku, na kuwa da muku, ‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.” Filibiyawa 4:6-8 “Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roko, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.” Zabura 50:15; “Ku yi kira gare Ni sa’ad da wahala ta zo, Zan cece ku, ku kuwa za ku yabe Ni.”
Bari mu dauki jarabawa daban-daban a matsayin matakala ne ta rayuwa ga sanin Ubangiji, a duk lokacin da muka shiga irin wannan yanayin. Shi ya sa ya kamata mu san Littafi Mai tsarki, muna yin bincike muna nazari da kuma addu’a dare da rana ba tare da sai wani ya fada mana me ke cikinsa ba. Domin rayuwa na nan ne kamar makaranta, a karshen kowane darasi malami yakan ba da jarabawa don ya gwada dalibansa ko sun fahimci abin da suka koya. Wanda ya ci nasara akan ba shi lambar yabo, sannan wanda ya fadi yakan maimata darasin ko ya samu lambar faduwa, hakan nan rayuwa take. Sai mu lura mu yi koyi da kowace irin jarabawa da muke fuskanta a rayuwarmu, muna rokon Ubangiji muna kuma gode maSa a kowane yanayi da muka samu kanmu a ciki.
Yakubu 1:2-4 “Ya ku ’yan uwana! Duk sa’ad da gwaje-gwaje iri-iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki kwarai. Domin kun san jarrabawar ban-gaskiyarku takan haifi jimiri. Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da komai ba.”
Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah Ya bar mu da rai da lafiya. Shalom.