Ubangiji Ya umarceni da in nemi Shugaban Kasa- Pastor Tunde Bakare

Shugaban Cocin Latter Rain Assembly da ke Jihar Legas, Pastor Tunde Bakare ya ce Ubangiji ne Ya sanar dashi cewa ya nemi Shugaban Kasa. Tuned Bakare ya sanar da hakan ne a lokacin taron ibadar sabuwar shekara day a gudana a Cocinsa. “Da misalin karfe hudu na safiyar Lahadi. Sai Ubangiji Ya ce mani ‘kada […]

Ubangiji Ya umarceni da in nemi Shugaban Kasa- Pastor Tunde Bakare

Shugaban Cocin Latter Rain Assembly da ke Jihar Legas, Pastor Tunde Bakare ya ce Ubangiji ne Ya sanar dashi cewa ya nemi Shugaban Kasa.

Tuned Bakare ya sanar da hakan ne a lokacin taron ibadar sabuwar shekara day a gudana a Cocinsa.

“Da misalin karfe hudu na safiyar Lahadi. Sai Ubangiji Ya ce mani ‘kada ka yi watsi da harkar siyasa, akwai sauran abun da ake bukata daga kai. Ka nemi Shugaban Kasa’. Don haka zan nema idan lokaci ya yi,” in ji Pastor Bakare.

Pastor Bakare ya kara da cewa, “Na so in bar wa kaina wannan maganar ba tare da sanar da kowa ba saboda wasu za su yi murna, wasu kuma za su Allah wadai. Amma ruhi mai tsarki ba zai bari in yi shiru ba.”