UEFA ta dage kulob din Galatasaray

Hukumar shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta dage kulob din Galatasaray da ke Turkiyya har tsawon shekara daya daga shiga kowace irin gasa da hukumar ta shirya.Hukumar ta ce ta yi haka ne saboda samun kulob din da laifi wajen kashe kudi ba bisa ka’ida ba, kuma ta yi biris da shawarar da […]

UEFA ta dage kulob din Galatasaray
UEFA ta dage kulob din Galatasaray

Hukumar shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta dage kulob din Galatasaray da ke Turkiyya har tsawon shekara daya daga shiga kowace irin gasa da hukumar ta shirya.
Hukumar ta ce ta yi haka ne saboda samun kulob din da laifi wajen kashe kudi ba bisa ka’ida ba, kuma ta yi biris da shawarar da ta ba ta na ta yi taka-tsan-tsan a kan yadda take kashe kudi.
A watan Janairun bana ne dai hukumar ta rubuta wa kulob din wasikar gargadi a kan yadda kulob din yake kashe kudi musamman wajen yin cefanen ’yan kwallo ba bisa ka’ida ba.  Sai ga shi kwatsam hukumar ta zartar da hukuncin dage kulob din har na tsawon shekara daya s shekaranjiya Laraba a wata sanarwar da ta fitar.
Idan za a tuna, a zagayen farko ne aka fitar da kulob din Galatasaray daga gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Cahmpions League) a bana.
Da wannan dagewa da aka yi wa kulob din yanzu ba zai halarci kowace irin gasa da hukumar ta shirya ba, kamar ta zakarun kulob-kulob na Turai ko gasar UEFA.  Sai dai kulob din zai cigaba da yin wasa ne a gasar rukunin Turkiyya da sauran kofunan da ake shirya wa a kasar.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa