UEFA ta dauke wasan karshe na ‘Champions League’ daga Rasha
Matakin ya biyo bayan kaddamar da hare-hare da Rasha ta yi a kam Ukraine.
Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) ta dauke wasan karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai wanda za a buga a birnin St Petersburg na kasar Rasha zuwa birnin Paris na kasar Faransa.
Matakin ya biyo bayan kaddamar da hare-hare da kasar Rasha ta yi ne a kan Ukraine ranar Alhamis.
- Matashiya ta maka mahaifinta a kotu saboda ya yi mata auren dole
- NAJERIYA A YAU: Yadda Rikicin Rasha da Ukraine Ya Dugunzuma ‘Yan Najeriya
Tun ranar ta Alhamis hukumar ta kira taron gaggawa, inda ta shiga tattaunawa a kan yiwuwar dauke wasan karshen daga Rasha.
Tun kafin fara gasar ta bana, UEFA ta fitar da birnin St Petersburg a matsayin wurin da za a buga wasan karshe.
Tuni aka fara nuna kin jinin fara yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine a wasannin gasar Europa da aka gudanar ranar Alhamis.