UEFA ta haramta wa Juventus shiga Gasar Zakarun Turai a bana

Mun yi bakin cikin hukuncin da UEFA ta yanke amma ba za mu daukaka kara ba.

UEFA ta haramta wa Juventus shiga Gasar Zakarun Turai a bana

Juventus

Hukumar Shirya Gasar Zakarun Turai ta UEFA, ta haramta wa Juventus halartar gasar cin kofin zakarun Turai na bana da kuma cin tarar kungiyar saboda karya dokar kashe kudi fiye da samun kungiya.

UEFA ta ce lamarin ya shafi hada-hadar da aka yi tsakanin shekarar 2012 zuwa 2019.

UEFA ta kuma ci tarar Chelsea tarar da ta saba wa dokar, sakamakon mika bayanan yadda ta kashe kudade ba yadda ya kamata ba.

Hukumar ta ce lamarin ya shafi hada-hadar da aka yi tsakanin shekarar 2012 zuwa 2019.

Haka zalika an ci tarar Juventus sama da yuro miliyan 19.90, yayin da aka ci tarar Chelase sama da yuro miliyan 10.

Kulob din na Italiya zai biya rabin tararsa ne kawai idan bayanan kudi na shekaru uku masu zuwa ya bi ka’ida, yayin da Chelsea ta riga ta amince ta biya kudin tararta.

Chelsea ta kashe sama da yuro miliyan 700 wajen sayen sabbin ‘yan wasa 19 tun lokacin da sabon mai kungiyar Todd Boehly ya kammala sayenta a watan Mayun 2022, amma tarar tasu na da alaka da lokacin da Roman Abramovich ke rike da kungiyar.

UEFA ta ce: “Bayan sayar da kulob din a watan Mayun 2022, an gano wanda ya mallaki kulob din, kuma an kai rahoto ga UEFA, kan yiwuwar rashin cikakkun bayanai kan yadda kungiyar ta kashe wasu kudade a baya.”

A yanzu dai hukumar kwallon kafa ta Italiya ta sanar da UEFA kungiyar da za ta maye gurbin Juventus a gasar cin kofin zakarun Turai.

Akwai yiwuwar Fiorentina, wadda West Ham ta doke ta a wasan karshe na bara, bayan da ta kare a matsayi na takwas a gasar Seria A ta maye gurbin kungiyar.

Tuhumar da ake wa Juventus ta biyo bayan tarar Yuro 718,000 a matsayin wani bangare na yarjejeniya da hukumomin kwallon kafar Italiya kan batun biyan albashin ‘yan wasa.

Tun da farko an yanke musu hukunci na rage maki 15 a watan Janairu amma kotun kolin wasanni ta Italiya ta soke hukuncin a watan Afrilu tare da ba da umarnin sake duba lamarin.

Juventus dai ta kare a matsayi na hudu wanda hakan ke nufinta cancanci shiga gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa da ba ta samu wannan hukunci ba.

A martanin da kungiyar ta fitar, Juventus ta ce ta amince da hukuncin UEFA kuma ba za ta daukaka kara ba.

Shugaban kungiyar Gianluca Ferrero ya ce: “Mun yi bakin cikin hukuncin da UEFA ta yanke, muna da yakinin sahihancin ayyukanmu da kuma sahihancin hujjojinmu.”

“Bugu da kari, mun yanke shawarar ba za mu daukaka kara kan wannan hukunci ba,” in ji Ferrero.

“Daukaka kararraki, mai yiwuwa zuwa wasu matakan shari’a, zai haifar mana da sakamako maraa tabbas da cinye mana lokaci, zai kara rashin tabbas game da yuwuwar halartar mu gasar zakarun Turai ta 2024/25.”

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara