UEFA ta haramta wa Mourinho wasanni 4 saboda zagin alkalin wasa
Ya yi zagin ne a wasan karshe na kungiyarsa da Sevilla
Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta haramta wa Manajan kungiyar kwallon kafa ta AS Roma, Jose Mourinho, taka rawa a wasanni hudu.
Matakin ya biyo zargin sa da aka yi da zagin alkalin wasa dan kasar Ingila, Anthony Taylor, yayin da kuma bayan kammala wasan karshe na gasar Europa League.
- Fada ya dawo ’yan mintuna bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan
- Za a yi wa Tinubu, Mataimakinsa, Gwamnoni da ’yan majalisa karin albashi
UEFA ta sanar da dakatarwar ce a cikin wata sanarwa da sashenta na ladabtarwa ya fitar da ta kunshi jerin matakan horo ga abubuwan rashin da’ar da aka yi a gasar Seria A.
Kungiyar Mourinho ta AS Roma dai ta sha kashi a wasan a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasanta da Sevilla, lamarin da ya kawo karshen tarinin da Manajan nata ya kafa a wasan.
Mourinho, wanda kuma tsohon Manajan Kungiyoyin Real Madrid da Chelsea ne, ya fusata a wasan bayan ya zargi alkalin shi da yi wa kungiyarsa son kai.
To sai dai bayan kammala wasan, Mourinho ya bi Anthony har wajen da ake ajiye ababen hawa, inda kyamarori suka nuna shi yana nuna alkalin wasan da hannu, yana zagin sa.
Bugu da kari, daga bisani lokacin da alkalin wasan yake shirin barin filin wasa na Budapest washegari, wasu fusatattun magoya bayan AS Romar sun kai masa farmaki a can.
Dakatarwar da aka yi wa Mourinho dai na nufin ba zai shiga wasanni hudu na rukunin da za a yi ba a kakar wasa ta badi.