Uganda ta kasa hukunta manyan barayinta – Rahoto
Wani rahoto da wasu cibiyoyin kare hakkin dan Adam suka fitar a ranar Litinin da ta gabata ya ce kasar Uganda ta kasa daukar matakin hukunta manyan jami’an gwamnatinta da aka samu da sace kudin talakawa, a daidai lokacin take kamawa da tsare masu ’yan rajin yaki da cin hanci da rashawa.Kamfanin Dillancin Labarai na […]
Wani rahoto da wasu cibiyoyin kare hakkin dan Adam suka fitar a ranar Litinin da ta gabata ya ce kasar Uganda ta kasa daukar matakin hukunta manyan jami’an gwamnatinta da aka samu da sace kudin talakawa, a daidai lokacin take kamawa da tsare masu ’yan rajin yaki da cin hanci da rashawa.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa wani bincike da kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Rights Watch (HURIWA) da Makarantar Nazarin Shari’a ta Yale suka gudanar ya gano cewa babu wani babban jami’in gwamnati, kamar minista ko wanda aka nada kan mukamin siyasa da aka taba daurewa a gidan kurkuku duk da dimbin binciken badakalar almundahana da aka rika yi shkekara da shekaru.
“Almundahana da kudin talakawa na matukar kawo kunci ga ’yancin jama’a a Uganda a shekaru da dama da suka shude. Kuma kudin tallafi daga kasashen waje da ya kai Dala miliyan 12 da dubu 700 (kimanin Naira biliyan biyu) aka sace a ofishin Firayiministan kasar a karshen bara. An ware kudin ne domin sake gina Arewacin Uganda da yakin shekara 20 ya daidaita da yankin Karamoja mafi talauci,” inji rahoton.
“Sai badakalar da ta shafi shirin kiwon lafiya da ta hada da karkatar da Dala miliyan 45 (kimanin Naira biliyan bakwai da rabi) daga Asusun Global Fund, domin yaki da cutar kanjamau da tarin fuka da maleriya a shekarar 2010, sai Dala miliyan 12 (kusan Naira biliyan biyu) daga wata cibiyar rigakafi mai suna Global Alliance for baccines and Immunisations a shekara 2006,” inji rahoton.
Binciken mai shafi 63 mai taken: “kyale babban kifi na ta ninkaya: Kasa hukunta manyan barayi a Uganda,” ya ce almundahana na iya jawo “manyan illoli” saboda sace dukiyar tallafi da ake ba da wa domin tabbatar da adalci wajen shari’a da kiwon lafiya da samar da ruwan sha da abinci da ilimi da sauransu.
Babbar mai bincike a Afirka ta kungiyyar HURIWA, Maria Burnett ta shaida wa manema labarai a Kampala wajen mika rahoton cewa: “Wannan gwamnati ta tsaya domin kawar da almundahana tun hawanta mulki a 1986, amma muna ganin yadda almundahana yake kara baje koli a kasar.” Ta ce a duk lokacin da batun almundahana ya je gaban kotuna Shugaba Musebeni kan fito bainar jama’a yana kalubalantar a kawo hujja a kai, kuma yana tallafa wa wanda ake tuhuma. “Yadda ya yi kane-kane a harkokin jama’a babban abin damuwa ne,” inji Burnett.