Ukraine ce mai laifi a yaƙin da ta ke yi da Rasha — Trump
Taron na Saudiyya wani mataki ne na nemo mafita game da yaƙin.

Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su.
Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a Saudiyya ba.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja
- ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa
A cewar Trump, Ukraine ce ta jawo wa kanta matsalar.
“Da ba ku fara wannan yaƙin ba, da kun cimma yarjejeniya tun farko,” in ji shi.
“Da ni ne, da na samo muku mafita, kuma babu wanda za a kashe.”
A Saudiyya, Rasha da Amurka sun fara tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin.
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce: “Ba za mu amince da dakarun Nato a Ukraine ba.”
Lavrov ya ce Rasha na son tattaunawa, amma ba za ta yarda da wata yarjejeniya da za ta bai wa Nato damar girke dakarunta a Ukraine ba.
A nasa ɓangaren, Zelensky ya mayar da martani da cewa Rasha ba abin dogaro ba ce.
“Rasha ba abin yarda ba ce. Dole ne a tilasta mata zaman lafiya.”
Trump ya kuma soki Ukraine kan rashin gudanar da zaɓe tun bayan fara yaƙin.
“Shin ’yan Ukraine ba za su iya fita su zaɓi shugabansu ba? An ɗauki tsawon lokaci ba a yi zaɓe ba.”
Ya ƙara da cewa Ukraine ta rasa goyon bayan jama’arta, yana mai iƙirarin cewa Zelensky ya rasa kashi huɗu cikin 10 na magoya bayansa.
A yayin da ake ci gaba da rikici, Amurka da ƙasashen Turai na ƙoƙarin samun mafita, amma Trump ya ce Amurka ba za ta tura dakarunta zuwa Ukraine ba.
“Idan Turawa suna son yin yaƙi, abu ne mai kyau, ina goyon baya,” in ji Trump.
“Amma Amurka ba ta da nasaba da wannan rikici.”
Taron Saudiyya dai na ɗaya daga cikin matakan tattaunawa tsakanin manyan ƙasashen don kawo ƙarshen wannan rikici, wanda ya haddasa asarar rayuka tun a shekarar 2022.