Ukraine ce ta harbo mana makami mai linzami — Gwamnatin Poland
Laifin ya rataya ne a kan Rasha saboda hare-haren da take kaiwa Ukraine.
Gwamnatin Poland da Kungiyar Tsaro ta NATO sun ce mai yiwuwa fashewar wani makami mai linzami da aka samu a kasar na tsaron sararin samaniyar Ukraine ne.
Sai dai sun ce Ukraine din ta harbo makamin ne a kokarin kare kanta daga harin da Rasha ta so kai wa kan wani gini na al’ummarta, saboda haka Moscow za a zargi alhakin harin saboda ita ta fara takalar yakin da ake yi tsakaninsu.
- An yi gwanjon kwallon da Maradona ya ci da hannu kan $2m
- ’Yan sanda sun kubutar da fasinjoji 8 da aka sace a Kuros Riba
Mutumin biyu ne aka samu rahoton mutuwarsu sakamakon fashewar makamin mai linzami a wani kauye da ke Poland wanda ya yi iyaka da kasar Ukraine.
Da yake jawabi a ranar Talata, Shugaba Andrzey Duda ya ce makamin samfurin kasar Rasha ne, sai dai ya kara da cewar har a zuwa wannan lokacin babu kwakwarar shaida akan wanda ya harbo shi, amma na fara bincike.
Makamin da ake magana ba namu ba ne —Rasha
Rasha dai tuni ta fidda bayani da ke musanta zargin harba wannan makami da Ukraine ke yi mata.
Kakakin gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya bayyana cewa, “babu wani dalilin shiga zaman tankiya, ya kamata ku sani cewa, kasar Poland ta mallaki dukkanin fasaha da kwarewa, kuma tana da na’urar kare kanta daga makamai mai linzami samfurin S. 300.
“Sannan dukkanin kwararru sun tabbatar da cewaa, makamin da ake magana a kai, ba na sojojin Rasha ba ne.”
Peskov ya kuma ce, ya kamata a daina cece-kuce, yana mai bukatar jama’a da su mayar da hankali kan martanin da ya fito daga Amurka biyo bayan wannan harin, wanda ya sha ban-ban da irin martanin da Poland ta mayar.
Kazalika gwamnatin Rasha ta gargadi mahukuntan Poland da su kiyaye lafuzzansu kan wannan batu mai cike da hatsari.
Yanzu haka gwamnatin Rasha ta kira Jakadan Poland da ke kasarta biyo bayan zargin da aka yi mata na kaddamar da harkin wanda ya kashe fararen hula biyu.
A halin yanzu dai mahukuntan na Poland na shirin kara tsaurara tsaro a sararin samaniyarsu tun bayan wannan hari da suka ce mai cike da barazana.
Kasashen Yamma sun kira taron gaggawa
Harin wanda ya sauka a kan guda daga cikin kasashen mambobin Kungiyar Tsaro ta NATO, ya assasa kiran taron gaggawa, wanda shugaban Amurka Joe Biden ya shugabanta, ya kuma tabbatar da cewar zai iya janyo mumunar ramuwar gayya daga kungiyar.
Sai dai shugabannin kasashen Yammacin Duniya sun yi watsi da fargabar a ranar Laraba, bayan da suka yi soma babatun cewa kazamin harin na makami mai linzami da aka kai a gabashin Poland na iya shelanta wani mummunan tashin hankali a yakin da Rasha ta kaddamar da Ukraine.
Shugabannin sun kira taron ne yayin da suka tsaka da gudanar da Taron Kungiyar Kasashe Masu Karfin Tattalin Arziki na G20 a birnin Bali na kasar Indonesiya.
Babu abin tayar da hankali —Poland
A kan haka ne Shugaban na Poland, Andrzej Duda ya ce babu wani abun tayar da hankali domin kuwa babu wasu dalilai da ke nuna wannan hari ya auku ne a matsayin takalar fada.
Duda ya ce, akwai yiyuwar Ukraine ta harba makami mai linzami tun na zamanin Soviet a wani abu da ya kira hatsarin da ba a so ba, ya kuma ce laifin ya rataya ne a kan Rasha saboda hare-haren da take kaiwa Ukraine.