Ukraine: Kwamitin Sulhun MDD ya goyi bayan yunkurin zaman lafiya

Sai dai kuma a lokacin jawabin, kwamitin sulhun ya kauce wa amfani da kalmar ‘yaki’, ‘rikici’ ko ‘mamaya’.

Ukraine: Kwamitin Sulhun MDD ya goyi bayan yunkurin zaman lafiya

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya goyi bayan yunkurin samar da zaman lafiya a rikicin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine, wanda ya zama matsala a duniya.

Bayanin farko na kwamitin kan rikicin ya nuna goyon baya ga kokarin da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, yake yi na neman mafita.

Karon farko ke nan da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wata sanarwar hadin gwiwa tun lokacin da aka fara yakin Ukraine, tare da bayyana “babban goyon baya” ga kokarin Mista Guterres na neman hanyar warware rikicin cikin lumana.

Sai dai kuma a lokacin jawabin kan yunkurin kawo zama lafiyan, kwamitin sulhun ya kauce wa amfani da kalmomin ‘yaki’, ‘rikici’ ko ‘mamaya’.

Amurka ta kara wa Ukraine makamai

Wannan na zuwa ne yayin da Amurka ta yanke shawarar tura karin Dala miliyan 150 na taimakon soji ga Ukraine, wanda ya kawo jimillar irin wannan taimakon da ba wa Ukraine zuwa Dala biliyan 3.8 tun lokacin da Rasha ta mamaye kasar.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce taimakon zai hada da karin makamai da wasu kayan aiki daga ma’aikatar tsaro, ba tare da yin cikakken bayani ba.

Blinken ya ce, “Za mu ci gaba da bai wa Ukraine makaman da sojojinta ke amfani da su yadda ya kamata don kare kasarsu da ’yancin ’yan uwansu.”

Ya kara da cewa taimakon sojan ya zo ne tare da sauran kokarin da Gwamantin Amurka ke yi na tallafa wa Ukraine da kuma matsa wa Rasha lamba.

A halin da ake ciki kuma, Ukraine ta ce an kwashe karin fararen hula daga cibiyar sarrafa karafa ta Azovstal da ke Mariupol, inda aka ceto karin fararen hula 50 a ranar Asabar.

‘Turjiyar farar hula’ a Mariupol

Amma Cibiyar Nazarin Yaki (ISW) ta ce “Watakila adawar farar hula ga mamayar Rasha na iya tarwatsa shirin Rasha na gudanar da bikin Ranar Nasara a Mariupol.”

Cibiyar ta ce baya-bayan nan ba za ta iya tabbatar da wani takamaiman ci gaban da Rasha ta samu kan harin da aka kai a kamfanin sarrafa karafa na Azovstal ba.

Amma wani jami’in tsaron Ukraine wanda ya yi gargadin “masu zagon kasa da sauran abubuwa masu laifi” gabanin Ranar Nasara ta Rasha.

Biden ya gana da Trudeau

A ranar Juma’a, shugaban kasar Amurka Joe Biden da Fira Ministan Canada, Justin Trudeau suka tattauna batun tallafin tsaro ga Ukraine, da kuma matakin da suka dauka na dora wa Rasha laifin mamaye kasar.

Yunkurin diflomasiyya don ceto mayakan Azovstal

Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy ya ce ana ci gaba da kokarin diflomasiyya domin ceto sojojin Ukraine da ke kare katafaren kamfanin sarrafa karafa na Azovstal da ke Mariupol.

“Masu shiga tsakani masu tasiri suna da hannu, jihohi masu tasiri,” in ji Zelenskyy a cikin jawabin da ya yi ta bidiyo, amma bai yi cikakken bayani ba.