Ukraine na so a mayar da tattaunawarta da Rasha birnin Kudus

Ukraine ta ce nan ne wurin tattaunawa mafi dacewa muddin ana son zaman lafiya

Ukraine na so a mayar da tattaunawarta da Rasha birnin Kudus

Zaman tattaunawar da aka tsakanin Firaministocin da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenski a Kyiv

Shugaban Kasar Ukraine, Volodimir Zolenskyy ya ce kasar Isra’ila na can na kokarin ganin ta shirya tattaunawa tsakanin kasarsa da Rasha a birnin Kudus.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi da ya yi wa mutanen kasar wanda aka watsa ta bidiyo a daren ranar Lahadi.

Ya ce, “Fira-Ministan Isra’ila, Mista Bennett, na ta kokarin ganin ya nemo kafar shirya tattaunawa. Muna yaba wa wannan kokarin nasa, saboda nan ba da jimawa ba za mu fara tattaunawa da Rasha, watakila a birnin Kudus.

“Ina ganin nan ne wurin da ya fi dacewa a tattauna in ana son samun zaman lafiya.”

A wani labarin kuma, kasar ta Ukraine ta yi watsi da kiran da ke yi mata na ta ba da kai bori ya hau wajen sallama birnin Mariupol.

Mataimakiyar Firaministan Ukraine Iryna Vereshchuk, ta ce ba ta ga dalilin da zai sa su yi saranda da birnin ba, inda ta bayyana bukatar a matsayin mamayar karfi da yaji daga Rasha.

A cewarta, dakarun Rashan na bukatar su da su da su yi saranda kafin su bari a kwashe fararen hula daga birnin