Ukraine: Rasha ta sanya makaminta na kare-dangi cikin shirin ko-ta-kwana

Makamin dai shi ne mafi hatsari a duniya

Ukraine: Rasha ta sanya makaminta na kare-dangi cikin shirin ko-ta-kwana

Kasar Rasha ta sanya makaminta na kare-dangi, kuma wanda ya fi kowanne hatsari a duniya cikin shirin ko-ta-kwana a ci gaba da yakin da take yi da Ukraine.

Makamin na Nukiliya mai suna RS-28 shi ne dai mafi hatsari a duniya kuma yanzu haka yana cikin shiri, kamar yadda shugaban kamfanin tsaron Rasha mai suna Roscosmos, Yury Borisov ya bayyana.

A cewar wani rahoton kafar yada labarai ta Eurasian Times, shugaban Roscosmos din ya bayyana haka ne yayin wata bita da hukumar leken asirin Rasha ta shirya ranar Juma’a.

Sai dai ya ki ya ce komai a kan takamaiman ranar da za a gwada amfani da makamin a cikin sanarwar.

Rasha dai ta fara kaddamar da makamin ne a karon farko a ranar 20 ga watan Afrilun 2022 a yankin Plesetsk Cosmodrome da ke Arkhangelsk na kasar.

An yi gwajin na farko ne wata biyu bayan kasar ta kaddamar da yaki a kan Ukraine.

A wannan karon dai, Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya yi gargadin cewa makamin zai yi dirar mikiya a kan duk wanda ya yi wa kasarsa barazana.