Ukraine ta kwace Karkhiv daga sojojin Rasha
Mazauna birnin Kharkiv suna komawa gidajensu bayan sojojin Rasha sun janye
Mazauna birnin Kharkiv na kasar Ukraine sun fara komawa gidajensu bayan sojojin Rasha da suka yi yunkurin mamaye birnin sun janye.
Gwammnan Kharkiv da ke Gabashin Ukraine, Oleh Synyehubov, ya ce sojojin kasar na ci gaba da kora dakarun Rasha, a yayin da mazauna birnin da suka tsere saboda yakin suka fara komawa gidajensu.
- Kar a yadda a shiga kakar zabe jami’o’i na rufe – Farfesa Alkali
- Gani ya kori ji: Hotunan muhimman abubuwa a wannan makon
Duk da haka, Synyehubov, ya yi gargadi cewa yanayin na da hadari, don haka jama’a da su rika rika yin la’akari da yanayin tsaronsu kafin su dawo birnin da zama.
A cewarsa, sojojin Rasha sun dasa nakiyoyi masu tarin yawa a yankin, kafin su janye.
Synyehubov ya kuma ce dakarun na Rasha ba su kai hari a birnin Kharkiv ba, sai dai wasu kauyuka da ke yankin.
“Saboda haka bai kamata a yi saurin sakin jiki ba, don haka ina kira ga jama’a da su yi gaggawar yin abin da ya dace da zarar sun ji sanarwa ko wata alama, sannan su daina fita kan tituna sai idan ya zama dole,” inji shi.