Ukraine za ta yi zaben jin ra’ayin jama’a kan shiga NATO
Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya ce kasar za ta gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a akan shigarta kungiyar kawancan tsaro ta NATO da zarar ta cika sharuddan shiga.Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin wata tattaunawa da ya yi da shugaban kasar Lithuania, amma bai yi karin haske ba kan batun. Sai dai bai bayyana […]
Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya ce kasar za ta gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a akan shigarta kungiyar kawancan tsaro ta NATO da zarar ta cika sharuddan shiga.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin wata tattaunawa da ya yi da shugaban kasar Lithuania, amma bai yi karin haske ba kan batun. Sai dai bai bayyana sharuddan ba. Kadayake, a makon jiya ne kasar Rasha ta bukaci kasar da ta ba ta cikakken tabbacin cewa ba za ta shiga kungiyar NATO ba.
kasar Ukraine dai ta kwashe shekara guda tana yakar ’yan aware masu samun goyon bayan Rasha.Har ila yau, masana na ganin cewa saboda rikici ya yi wa kasar dabaibayi da wuya kungiyar ta yi maraba da ita.
Kakakin Shugaban kasar Rasha Dmitry Peskob ya zargi kungiyar da karya alkawarin da ta dauka ta hanyar shiga iyakokin Rashar. Ya bayyana wa BBC kungiyar ta kokarin rusha raba-daidai kasashen da aka tsakanin Rashar da Yammacin Duniya.
A shekarar 1999 ne kasashe uku da suka balle daga Tarayyar Sobiet suka shiga kungiyar NATO.Hakazalika, a shekarar 2004 ma an samu hakan,inda ciki har da kasr Lithuania. Hakan ya sa a ranar Litinin da ta gabata kasar da wasu kasashe da ke cikin kungiyar suka aike da taimakon sojoji zuwa Ukraine.
Rikici ya ci gaba a yankin gabashin Ukraine duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka cimma a ranar 5 ga watan Satumbar da ya wuce. Mako takwas tun bayan sanya hannu a yarjejeniyar akalla mutum 1,000 ne suka rasa rayukansu, a cewar Ofishin Kare Hakkin dan Adam na Majalisar dinkin Duniya.