Umar FK ya fice daga PDP zuwa APC da magoya bayansa a Gombe
Ɗan siyasar ya ce jam’iyyarsa ta PDP ta gaza magance matsalolin shugabanci da take fama da shi.
Siyasar Jihar Gombe ta ƙara ɗaukar zafi yayin da fitaccen ɗan siyasar nan, Umar Faruk FK, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da dimbin magoya bayansa, tare da komawa APC.
FK, ya bayyana cewa PDP ta gaza bayar da shugabanci nagari a jihar, shi ya sa ya yanke shawarar barin ta.
- 2027: ’Yan adawa na ƙoƙarin sanya APC fara kamfe da wuri — Tinubu
- Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin Kofa
Ya ce ya mara wa Gwamna Inuwa Yahaya baya bisa ayyukan ci gaba da ya ke gudanarwa.
“Marar kishin Gombe ne kawai ba zai ga nasarorin da gwamnatin Inuwa Yahaya ke samu ba,” in ji Umar FK.
Ya ƙara da cewa shi da magoya bayansa za su mara wa gwamnan baya a shirin neman kujerar Sanatan Gombe Arewa a 2027.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, da shugaban APC a Ƙaramar Hukumar, Alhaji Abubakar Danladi, sun tarbi FK cikin farin ciki, inda suka ce dawowarsa babbar nasara ce da za ta ƙara APC ƙarfi a jihar.