Umar Rayyan, a Abuja Ko za ka gabatar da kanka? Sunana Kabiru Sani Kamba, amma wasu na kira na Sharifin Waqa, wannan ba ya rasa nasaba da basirata wajen hikaito waqa. An haife ni a shekarar 1979 a Qaramar Hukumar Kamba da ke Jihar Kebbi. Na yi makarantar

Ko za ka gabatar da kanka? Sunana Kabiru Sani Kamba, amma wasu na kira na Sharifin Waka, wannan ba ya rasa nasaba da basirata wajen hikaito waka. An haife ni a shekarar 1979 a karamar Hukumar Kamba da ke Jihar Kebbi. Na yi makarantar haddar Alkur’ani mai girma kusan shekara 11 kafin na haddace.Mahaddaci ne […]

Umar Rayyan, a Abuja Ko za ka gabatar da kanka? Sunana Kabiru Sani Kamba, amma wasu na kira na Sharifin Waqa, wannan ba ya rasa nasaba da basirata wajen hikaito waqa. An haife ni a shekarar 1979 a Qaramar Hukumar Kamba da ke Jihar Kebbi. Na yi makarantar
Umar Rayyan, a Abuja Ko za ka gabatar da kanka? Sunana Kabiru Sani Kamba, amma wasu na kira na Sharifin Waqa, wannan ba ya rasa nasaba da basirata wajen hikaito waqa. An haife ni a shekarar 1979 a Qaramar Hukumar Kamba da ke Jihar Kebbi. Na yi makarantar

Ko za ka gabatar da kanka?

Sunana Kabiru Sani Kamba, amma wasu na kira na Sharifin Waka, wannan ba ya rasa nasaba da basirata wajen hikaito waka. An haife ni a shekarar 1979 a karamar Hukumar Kamba da ke Jihar Kebbi. Na yi makarantar haddar Alkur’ani mai girma kusan shekara 11 kafin na haddace.
Mahaddaci ne kai ke nan?
kwarai kuwa.
Ya bangaren karatun boko fa?
A gaskiya daga bakin karatun sakandare na tsaya.
Me ye ya ja hankalinka zuwa sana’ar waka?
Lokacin da na bar makarantar hadda na koma garin Zariya da zama kimanin shekara 11 da suka wuce ke nan. Daga nan ina karatun littattafai sai na fara karatun Diwani da wake-wake da Ishiriniyya da sauransu. To daga nan ne sai na zo na kafa wani kamfanin wasa a nan Abuja. A wannan gabar ne sai na ce bari in kwatanta rera waka. Ashe nan Allah Ya kaddari abincina yake. Amma ni wakokin siyasa kawai nake yi.
Kamar wane dan siyasa ka fara yi wa waka?
Wanda na fara yi wa waka a gaskiya shi ne Janar Muhammadu Buhari, wato sabon Shugaban kasa amma tun kimanin shekara 12 da suka wuce. Saboda ni mai kaunarsa ne sosai kuma har gobe ina yi masa waka.
Bayan Shugaba Buhari, akwai wasu ’yan siyasa da ka yi wa waka?
kwarai kuwa. Akwi irin su tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Sa’idu Nasamu dakingari da sabon Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Lawali Garma da Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero da Sabon Sarkin Muhammadu Sanusi na II da sauransu.
Me ya sa wakokinka suka takaita ga ’yan siyasa da sarakuna?
Abin da ya sa wakokina suka fi karfi wajen ’yan siyasa, kauna ce da ra’ayi.
Wane kalubale kake fuskanta ta bangaren sana’arka?
Akwai su da dama. daya daga ciki shi ne za ka iya zuwa matsayinka na dan takara mai neman wani mukami, idan mukarrabansa sun san mawaka, sai su bukaci mu yi wa mai gidansu waka. Daga nan mu za mu yi aikin domin kishi da nuna kauna, amma daga nan idan ka ba su kwafin wakar, sai ka ga suna kyashin su hada ka da mai gidan nasu domin watakila suna bakin cikin abin da za ka samu. Har ila yau, wani babban kalubale da muke fuskanta shi ne na satar fasaha.
Wadanne nasarori ka samu daga harkar waka?
Tun da na fara sana’ar, wakata ta farko ce kawai ban samu kudi ba sosai, amma duka wadanda suka biyo bayanta abin ba a cewa komai. Har ila yau, a harkar waka na samu filaye har guda biyu da sauran alherai.
Wace waka ce Bakandamiyarka?
Gaskiya ba wakar da na fi kauna irin wata guda wadda na yi wa Shugaba Buhari. Abin da nake cewa a wakar kuwa shi ne: “Taro jama’a mu zabi CPC jam’iyyar Buhari mai gaskiya.”
Me ya sa ba ka yin wakokin soyayya?
Na taba yin wakar soyayya sau daya, amma daga nan ban bari wakar ta fita ba. Tana nan a boye a wurina. Babu wanda ya taba sauraronta bayan ni.
Me ya sa? Ba ta yi dadi ba ne?
Saboda abu guda ne. Sau da yawa an sha ce mini in yi wakar soyayya amma sai in ki. Ganin cewa rana daya kwatsam na yi, sai na yanke shawarar na boye kayana.
Wace ce ka yi wa wakar?
Na yi kan wata yarinya ce. Ka san yadda nake ganin yadda mawakan soyayya suke yi sai na ga kamar almara amma sai abin ya zo ya faru a kai na. Yarinya dai ina son ta sosai, muna soyayya kwarai. Kwatsam wata rana sai na gan ta tare da wani abokina. Ka ji abin da ya sa ni rewa wakar soyayya ta farko.
Kana da wani buri a halin yanzu?
Babban burina shi ne in samu wata sana’ar bayan harkar waka.
Ya batun iyali fa?
Na taba yin aure amma a halin yanzu mun rabu. Kodayake, a yanzu haka na yi haramar kara yin wani auren.