Umar Sa’idu Tudun Wada: Ba rabo da gwani ba…
Fiye da wata biyu ke nan da rasuwar Malam Umar Sa’idu Tudun Wada, (Dan Masanin Tudun Wada), wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Lahadi 30 ga Yunin 2019 sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a garin Kura a hanyarsa ta dawowa daga Abuja. Marigayi Umar Sa’idu Tudun Wada, fitacce kuma kwararren […]
Fiye da wata biyu ke nan da rasuwar Malam Umar Sa’idu Tudun Wada, (Dan Masanin Tudun Wada), wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Lahadi 30 ga Yunin 2019 sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a garin Kura a hanyarsa ta dawowa daga Abuja.
Marigayi Umar Sa’idu Tudun Wada, fitacce kuma kwararren dan jarida ne da ya yi fice wajen yin hidima ga al’umma da ya samu kyakkyawar shaida lokacin da yake raye kan iya mu’amala da jama’a da karamci. Mutum ne mai tausayi da kokarin jawo mutane a jiki musamman wadanda suke aiki a karkashinsa. Ya kasance jigo wajen dora ma’aikatan gidan jarida ko rediyo don koyon aikinsu.
Rasuwarsa ta zamo babban rashi ba ga iyalainsa ko ’yan uwa abokan arziki ko ’yan jarida kadai ba, babban rashi ne ga al’ummar duniya, ganin yadda labarin rasuwarsa ta karade duniya tare da sanya alhini a zukatan jama’a. Kuma ya samu shaidar da muke fatan ta kai kabarinsa tare da tabbatar da rahama gare shi.
Halaye nagari na marigayin, ya sa fadar Hakimin Tudun Wada ta nada shi a sarautar Dan Masanin Tudun Wada sakamakon gudunmawar da ya bai wa yankin, Jihar Kano da kasa baki daya.
Ba shakka marigayin ya samu kyakkyawar shaida ta yadda mutane da dama suka gwammace su kasance suna kushewa. Allah Ya sa mu yi kyakykyawar cikawa da samun shaida ta mu’amala da halaye irin na dan uwanmu, abokin aikinmu da ya koma ga Mahallacinsa.
Na kasance daya daga cikin ’yan jarida da suka koyi wasu muhimman abubuwa daga gare shi da suke taimaka mini wajen gudanar da aikin jarida. A shekarar 2003 na yi aiki a karkashinsa lokacin yana mawallafin jaridar Factual Weekly ni kuma ina mai dauko masa rahoto daga Jihar Jigawa. Kullum abin da ya ke ba ni shawara shi ne in rike mutuncina da na aikin jarida ta hanyar dauko sahihan labarai masu inganci ba tare da yin barazana ko tsoratarwa ko hantarar mutane a yayin gudanar da aikina ba.
Sannan yana yawan fada mini cewa in rike gaskiya tare da sanin darajar mutane a aikin jarida wanda zai sa a yi koyi da ni. Kullum nakan tuna wadannan nasihohi da marigayin ya yi mini, kuma cikin hukuncin Allah na ga amfaninsu da na yi aiki da su.
An haifi marigayi Umar Sa’id Tudun Wada a 1960, a Karamar Hukumar Tudun Wada da ke Jihar Kano. Ya yi makarantar firamare a garin Tudun Wada, ya halarci Kwalejin Rumfa da ke Kano wadda a wancan lokaci ake kira da Kwalejin Gwamnati. Bayan kammala makarantar Rumfa ce ya wuce Jami’ar Bayero, inda ya yi karatun Diploma a bangaren Harkokin Mulki (Public Administration). Daga bisani ya sake komawa Jami’ar Bayero ya yi karatun Babbar Diploma a kan ci gaban kasa, a kan harkokin ci gaban kasa.
Jim kadan bayan ya kammala makarantar sakandire marigayi ya fara aiki, inda ya fara da koyarwa na tsawon shekara daya. Daga baya ya tsunduma harkar aikin jarida a 1980, inda ya fara da Gidan Talabijin na Kasa (NTA) da ke Kano. Ya kwashe shekara uku yana aiki da NTA, daga bisani ya koma Gidan Talabijin din Jihar Kano (CTB), wanda a yanzu ya koma ARTB. Bayan ya shafe shekara 18 a gidan talabijin na CTB, sai ya yi ritaya yana matsayin Edita.
Ya kuma taba zama wakilin Gidan Rediyon Jamus, a matsayin mai aika musu da rahoto daga Kano, a daidai lokacin da ya kasance Editan Mujallar Concern. Tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya taba nada shi Mataimakin Daraktan Watsa Labarai a 1999 zuwa 2003. A shekarar 2003 ne aka bude gidan Rediyon Freedom, inda aka nada marigayin Mataimakin Janar Manaja zuwa shekarar 2006, daga baya Muryar Amurka (BOA) suka bukaci ya je ya yi aiki da su, kuma ya je ya yi aiki da su na tsawon shekara uku da rabi.
A shekarar da Janar Manajan Rediyon Freedom, Malam Umar Dutse Muhammad ya rasu sai manya Daraktocin Hukumar Gidan Rediyon suka bukaci marigayi Umar S. Tudun Wada ya dawo don dorawa daga inda marigayi Dutse ya tsaya a sha’anin tafiyar da aiki tunda Allah Ya sa da shi aka bude gidan.
Sauran ayyukan da marigayin ya yi sun hada da aiki da gidan Rediyon Jamus (Radio DW) da gidan Rediyon Dandalkura da ke Jihar Borno.
Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya nada shi Manajan Daraktan Gidan Rediyon Kano daga shekarar 2015 zuwa 2019. Akwai yakinin cewa, yana daya daga cikin wadanda Mai girma Gwamna zai mayar kan kujerunsu sakamakon jajircewa, gaskiya, kwarewa da kuma sanin makamar aiki da marigayin ke da shi a wannan fanni na aiki jarida, amma sai Allah Ya yi naSa ikon.
Marigayi Umar shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Editoci ta Kasa (NGE), a zaben da aka gudanar a watan Mayun 2019, yana daya daga cikin wadanda suka lashe zabensu ba hamayya. Wannan ya faru bisa irin kwarewa da sanin makamar aiki da marigayin ke da ita a fannin aikin jarida da kuma iya mu’amala da jama’a da kokarin kwatanta gaskiya da adalci a duk inda ya samu kansa.
Fatarmu Allah Ya kai rahama kabarinsa tare da bai wa iyali da ’yan uwa da abokan arziki da sauran al’ummar Musulmi hakuri. Ya rasu ya bar matan aure uku da ’ya’ya sama da 20.
Aliyu Dangida, shi ne Mawallafin Mujallar Mahangar Arewa, kuma ya rubuto ne daga Jihar Kano.
za a iya samunsa ta: (08033195532 ko [email protected]