Umar Tsauri ya kai dauki ga jama’ar Sabuwa da Faskari
dan siyasar nan na Jihar Katsina Alhaji Umar Abdullahi Tsauri da aka fi sani da Alhaji Tata ya kai dauki ga al’ummomin kananan hukumomin Sabuwa da Faskari da ’suka hadu da ta’addancin yan fashin shanu a makon shekaranjiya.Alhaji Abdullahi Tsauri wanda ya kai tallafin a garuruwan Marabar Maigora da Maigora da Sabuwa da kuma Faskari […]

dan siyasar nan na Jihar Katsina Alhaji Umar Abdullahi Tsauri da aka fi sani da Alhaji Tata ya kai dauki ga al’ummomin kananan hukumomin Sabuwa da Faskari da ’suka hadu da ta’addancin yan fashin shanu a makon shekaranjiya.
Alhaji Abdullahi Tsauri wanda ya kai tallafin a garuruwan Marabar Maigora da Maigora da Sabuwa da kuma Faskari ya ba jama’ar garuruwan tallafin kayan abinci da suka hada da buhunan shinkafa 300 da na masara 300 da tanti-tanti dubu daya da tabarmi 1000 da bandir din shadda 1000 da kuma na atamfa 1000.
Baya ga haka Alhaji Tata ya ba iyalan kowane gida da harin ya rutsa da su tsabar kudi Naira dubu dari dari don saukaka musu halin kunci da harin ya jawo musu.
Da yake mika tallafin Alhaji Abdullahi Tsauri ya nemi jama’ar da hare-haren suka shafa su mayar da lamarin ga Allah kuma su dauki hakan a matsayin wata jarrabawa.
Ya roki Allah Ya kiyaye sake aukuwar irin wannan harin a yankin, inda ya yi kira ga masu hannu da shuni da kungiyoyi da sauran masu zuciyar taimako su taimaka wa jama’ar yankunan don farfado da rayuwarsu daga wannan hari da suka samu kansu a ciki.
Alhaji Tata ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su tashi tsaye domin magance hare-haren da ke aukuwa a yankunan jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara da ake jingina su ga masu satar shanu.
Jama’ar yankin sun mika godiya ga Alhaji Tata inda suka bayyana cewa wannan shi ne taimako mafi girma da suka taba samu daga gwamnati ko wani mutum a tarihinsu.
“Tunda muke ba mu taba samun tallafi daga gwamnati ko wani mutum irin wannan karo ba. Don haka babu abin da za mu ce da wannan bawan Allah Alhaji Umar Tata sai Allah Ya saka masa da alheri,” inji daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin da ya nemi a sakaya sunansa.