Buhari ya ziyarci kabarin Manzon Allah (SAW)

Buhari ya ziyarci kabarin Manzon Allah (SAW) da ke birnin Madina na kasar Saudiyya a ziyar aikinsa ta karshe a matsayin shugaban kasa.

Buhari ya ziyarci kabarin Manzon Allah (SAW)

Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci kabarin Manzon Allah (SAW) da ke birnin Madina na kasar Saudiyya a ziyar aikinsa ta karshe zuwa kasar matsayin shugaban kasa.

Mako bakwai kafin saukarsa daga mulki, Buhari ya sauka a Filin Jirgi na Yarima Mohammad Bin Abdulaziz  da ke  birnin Madina a yammacin ranar Talata domin ziyarar aikin na kwana takwas a kasar Saudiyya.

Mataimakin Gwamnan Madina, Sa’ud Khalid Al-Faisal ne ya tarbi Buhari, daga nan suka wuce Masallacin Manzon Allah (SAW) inda Buhari ya yi sallah ya ziyarci ga kabarin Manzon Allah (SAW).

Bayan kammala ziyarar aikin, Buhari zai gudanar da ibadar Umara a Masallacin Harami da ke birnin Makkah, kafin ya dawo gida Najeriya a jajibirin Karamar Sallah.

Wannan ziyarar aikin da umarar za su kasance na karshe da Buhari zai kai kasar Saudiyya a matsayin shugaban kasa.

A ranar 29 ga watan Mayu mai kamawa ne Buhari zai sauka daga mulki bayan kammala wa’adinsa na biyu a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya.

Kawo yanzu kwanaki 47 suka rage ya mika mulki ga magajinsa, Asiwajo Bola Ahmed Tinubu.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50