Umarce-umarce da dokoki

Sa’ar da ka zauna cin abinci tare da babban mutum, ka tuna da yadda yake. Idan kai mai son ci da yawa ne sai ka kanne. Kada ka yi hadamar kyakkyawan abincin da yake gabanku, zai yiwu wayo yake so ya yi maka. Ka zama mai isasshiyar hikima, kada ka gajiyar da kanka garin kokarin […]

Umarce-umarce da dokoki
Umarce-umarce da dokoki

Sa’ar da ka zauna cin abinci tare da babban mutum, ka tuna da yadda yake. Idan kai mai son ci da yawa ne sai ka kanne. Kada ka yi hadamar kyakkyawan abincin da yake gabanku, zai yiwu wayo yake so ya yi maka. Ka zama mai isasshiyar hikima, kada ka gajiyar da kanka garin kokarin neman dukiya. Kudinka suna iya karewa kamar kiftawar ido, kamar suna da fika-fikai su tashi kamar gaggafa. Kada ka ci abincin marowaci, ko ka yi hadamar kyakkyawan abincin da ya sa a gabanka. Zai ce, “Bari a kara maka,” amma ba haka yake nufi ba. Kamar gashi yake a cikin makogwaronka. Za ka harar da abin da ka ci, dukan dadin bakinka zai tafi a banza. Kada ka yi wa wawa magana irin ta hazikai, gama ba zai yaba da maganarka ba. Kada ka kuskura ka kawar da shaidar iyaka, ko ka kwace gonar marayu. Ubangiji Mai iko Shi ne kariyarsu, Shi zai yi magana dominsu. Ka mai da hankali ga malaminka, ka koyi dukkan abin da kake iyawa. Kada ka bar yaro ba horo, gama ko ka doke shi ba za a kashe shi ba. 14 Lallai ne za ka ceci ransa. Dana, idan ka zama mai hikima zan yi murna kwarai. Zan yi murna idan na ji kana fadar magana da hikima. Kada ka yi kyashin masu aikata zunubi tsoron Ubangiji kadai za ka sa a gaba. Idan haka ta samu za ka yi farin ciki nan gaba. Ka saurara, ya dana! Ka zama mai hikima. Ka yi tunani mai zurfi a kan hanyarka. Kada ka zauna da mashayan ruwan inabi, ko masu hadama. Gama bugaggu da ruwan inabi da masu zarin ci za su zama matalauta. Idan iyakar abin da kake yi daga ci sai barci ne, nan da nan za ka ga kana saye da tsummoki. Ka kasa kunne ga mahaifinka, gama ba dominsa ba, da ba ka, sa’ar da mahaifiyarka ta tsufa ka nuna mata godiyarka. Gaskiya da hikima da ilimi da hankali, sun cancanta a saye su, komai tamaninsu. Mahaifin adali yana da dalilin yin murna. Zai yi fariya a kan da mai hikima. Ka sa mahaifinka da mahaifiyarka su yi fariya da kai, ka sa mahaifiyarka farin ciki. Dana ka mai da hankali sosai, irin zamana ya zamar maka kyakkyawan misali. Karuwa da mata mazinata, tarkon mutuwa ne su. Sukan labe su jira ka kamar mafasa, suna sa mutane da yawa su zama marasa aminci. Wa ake yi wa kaito? Wa yake da bakin ciki? Wane ne mafadaci? Wa yake yin guna-guni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan ido? Sai rikakken mashayi wanda yake gaurayar ruwan inabi. Kada ka bar ruwan inabi ya jarabce ka, koda yake jawur yake, har kana iya ganin kanka a cikin kokon, yana kuwa da kyan gani sa’ar da kake motsa shi. Kashegari za ka ji kamar maciji mai dafi ne ya sare ka. Idanunka za su rika gane-gane, ba za ka iya tunani ko ka fadi magana sosai ba. Za ka ji kamar kana can cikin teku, jirin teku na dibarka kana lilo a kan rufin jirgin ruwa da yake tangadi. Za ka ce, “Lallai an doke ni, sosai an daddoke ni amma ban san lokacin ba, me ya sa ban farka ba? Ina bukatar in kara sha.”

Kada ka ji kyashin mugaye, kada ka yi kokarin yin abota da su. Duk tunaninsu na yin mugunta ne, a duk lokacin da suka bude bakinsu sai sun cuci wani. An gina gidaje a kan harsashin hikima da fahimta. Ta wurin ilimi a kan kawata dakuna da kyawawan kayayyaki masu tamani. Mai hikima kakkarfa ne, eh, mai ilimi yana dada karfi. Ban da wannan ma, dole ne ka shisshirya a natse kafin ka kama yaki. Bisa ga shawarwarin da za ka samu ne za ka yi nasara. Kalmomi masu hikima sun yi wa wawa zurfin ganewa kwarai, ba ya da ta cewa sa’ar da ake magana a kan muhimman abubuwa. Idan a koyaushe shirye-shiryen mugunta kake, za ka yi suna a kan kuta tashin hankali. Kowace irin dabarar da wawa yake tunani a kanta zunubi ne. Jama’a suna kin mutum mai rainiko. Idan ba ka da karfi a lokacin hargitsi, hakika ka tabbata marar karfi.

Kada ka ji nauyin ceton wanda ake janye da shi zuwa inda za a kashe shi. Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah Ya sani, Yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, Ya kuwa sani. Yakan saka wa mutane a kan abin da suke aikatawa. Dana, ka sha zuma gama tana da kyau. Kamar yadda kakin zuma yake da zaki a harshenka, haka ilimi da hikima suke da amfani ga ranka. Ka same su, a gaba za ka yi farin ciki. Kada ka shirya dabarun yi wa amintacce kwace, ko ka kwace masa gidansa, wannan mugunta ce. Ko sau nawa amintaccen mutum ya fadi, ba abin damuwa ba ne, gama a koyaushe zai sake tashi, amma masifa takan hallaka mugaye. Kada ka yi murna sa’ar da bala’i ya aukar wa makiyinka. Ubangiji zai sani in kana murna, ba kuwa zai so haka ba, mai yiwuwa ne ba zai hukunta shi ba. Kada ka damu saboda mugaye, kada ka yi kyashin masu aikata abin da ba daidai ba. Gama mugun mutum ba ya da sa zuciya, ba abin da zai sa zuciya a kansa nan gaba.

Dana, ka ji tsoron Ubangiji, ka kuma ji tsoron sarki, kada ka yi harkar komai da mutanen da suka tayar musu. Irin wadannan mutane sukan hallaka farat daya. Ka taba yin tunani a kan bala’in da Allah ko sarki sukan aukar?

(Karin Magana 23,24)