Umarnin da rundunar soja ta bayar na sojoji su koyi manyan harsuna uku ya dace?

A kwanakin baya ne rundunar sojin Najeria ta bayar da umarnin cewa dukan sojojin kasar su koyi manyan yarukan kasar nan. Wannan sanarwar ta janyo cece-kuce a tsakanin mutane. Hakan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ta bakin mutane, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:   Tsarin zai taimaka wa harkokin tsaro -Hamisu […]

Umarnin da rundunar soja ta bayar na sojoji su koyi manyan harsuna uku ya dace?

A kwanakin baya ne rundunar sojin Najeria ta bayar da umarnin cewa dukan sojojin kasar su koyi manyan yarukan kasar nan. Wannan sanarwar ta janyo cece-kuce a tsakanin mutane. Hakan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ta bakin mutane, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:

 

Tsarin zai taimaka wa harkokin tsaro

-Hamisu Kadade

Hussaini Isah, Jos

 

Malam Hamisu Adamu Kadade; ‘’A gaskiya wannan shiri ya yi daidai, domin sau tari idan a kan dauko soja daga kudancin kasar nan aka kawo shi Arewa, idan bai iya hausa  ba, ya kan samu matsaloli wajen gudanar da ayyukansa na tsaro. Haka kuma idan aka dauki soja daga Arewa a kai kudancin kasar nan, idan bai iya yaren ibo ko yarbanci ba, ya kan sami irin wadannan matsaloli.  Sau tari idan wata matsala ta taso sai kaga soja ya dauki matakin da bai dace ba, saboda rashin sanin harshen mutanen wajen da aka turo shi. Babu shakka idan aka dauki wannan mataki na soja ya koyi daya daga cikin manyan harsunan Najeriya guda uku zai taimaka wajen fahimtar juna musamman kan aikin harkokin tsaro a kasar nan. Wannan tsari ya yi daidai kuma zai samar da cigaba.”

 

Wannan tsari ne mai kyau –Manu Idris

Hussaini Isah, Jos

 

Manu Isah Idris; ‘’Wannan tsari ya yi daidai domin zai taimaka sosai wajen gudanar da ayyukan tsaro a kasar nan. Musamman idan aka dubi rashin zaman lafiyar da ake fama da shi a yankin Arewa maso Gabas da kuma yankin Neja Delta. Idan sojojinmu suka koyi wadannan manya harsuna guda uku wato hausa,yarabanci da ibo zasu ji dadin gudanar da ayyukansu na tsaro. Misali idan aka kawo soja ibo yankin arewa masu gabas kuma yana jin harshen hausa zai fi jin dadain gudanar da aikinsa. Haka kuma idan aka kai soja bahaushe yankin ibo ko yankin Neja Delta ko yankin yarbawa, idan ya koyi harshen ibo ko yarbanci zai fi jin dadin gudanar da aikinsa. Don haka wannan tsari ne mai kyau kuma zai taimakawa sojoji wajen gudanar da ayyukansu.”

 

Wannan abu ne mai kyau– Ozor Linus Ozor

Daga Umar Akilu Majeri,Dutse

 

Mista Ozor Linus Ozor Tsohon Shugaban kungiyar Igbo mazauna Jihar Jigawa:  “Tilasta wa sojojin Najeriya su koyi yaruka uku abu ne mai kyau. Dama ai ya dace duk dan Najeriya ya iya yaruka manya uku na Najeriya, misali kaga ni Ibo ne, amma na iya Hausa da Yarabanci bayan yarena na Ibo wanda da shi na taso. 

Amma a shawarata bai kamata a tilastawa wadanda suke cikin aikin sojan a yanzu ba, kamata ya yi a dauki malaman yarukan nan uku su koyar da su, sai ayi wata doka da za ta sanya duk wadda yake da sha’awar shiga aikin soja tilas ya koyi yaruka uku manya na Najeriya kafinma adaukeshi aikin sojan Shi wannan al’amari da Gwamnatin Tarayya take kokarin aiwatarwa abu ne da ya dace domin zai taimaka wajen ingantar zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasar nan kuma hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a Najeriya da inganta zamantakewa tsakanin sojojin kasar.”

 

 

Zai yi wahalar gaske – Nusaiba Suleiman

Isiyaku Muhammaed

 

Nusaiba Suleiman: “Gaskiya zai yi wahalar gaske yanzu wai a ce za a tilasta wa sojoji su koyi wani yare. Da wanne za su ji, da aikin ko koyon wani yare. Aikin soji akwai wahala matuka. kullum suna cikin aiki. idan har da gaske ake yi, to sai dai a fara koyar da harsunan a makarantun Sakandiri, sannan kuma a koyar da wadanda suke samun horo a matakin farko na shiga aikin soja. Amma idan har mutum ya riga ya fara aiki, to tsayar da shi domin wai ya koyi wani yare zai yi wahala.”

 

 

Abu ne mai kyau idan an yi shi yadda ya dace

– Adamu Muhammed Idris

Isiyaku Muhammed

 

Adamu Muhammed Idris: “wannan tsari ne mai kyau, amma idan anyi tsarin yadda ya kamata ke nan. Yawanci za ka ga an kawo tsari mai kyau a rubuce ko kuma a magana, amma idan aka zo wajen aiki, sai kawai ka ga ya shiririce. Mun yi zama a Kudancin kasar nan, kuma na san cewa iya magana da harshensu zai yi amfani wajen aiki mai kyau.”

 

 

Ya dace – Alhaji Ibrahim Shuwarin

Daga Umar Akilu Majeri,Dutse

 

Sunana Alhaji Ibrahim shuwarin mai shagon cosmetic : “Wannan abu ne da ya dace Gwamnatin Tarayya ta yi domin zai kawo hadin kan sojojin Najeriya kuma saboda aikinsu na tsarone, idan mutun ya je aiki inda ba ya jin harshensu, batagari za su iya cutar da shi, amma idan ya na jin yarensu, babu yadda za ayi a cuce shi. Saboda haka wannan mataki na tilasta wa sojoji su iya manyan yaruka uku na Najeriya, abu ne da ya dace, amma kamata ya yi a sami kwararrun malaman makaranta wadanda suke jin harshen guda uku su rika koyar da sojojin. Kuma tun lokacin da suke samun horo a wajen bayar da horo na deport da ke Zariya, a tabbatar an tsaya tsayin daka wajen ganin sun koyi yaran kafin a turasu wajen aiki.”