Umarnin da Tinubu ya ba wa shugabannin tsaro

Tinubu ya ce dole jami’an tsaro su je filin daga su murkushe duk wata barazanar tsaro, tare da ba su cikakkiyar kulawa da isassun kayan aiki

Umarnin da Tinubu ya ba wa shugabannin tsaro

Tinubu da shugabannin tsaro, a lokacin zaman farko da ya yi da su bayan zamansa shugaban kasa. (Hoto: Fadar Shugaban Kasa).

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gargadi shugabannin tsaro cewa kada su kuskura a samu wata rigima a tsakanin hukumominsu, domin gwamnatinsa ba za ta lamunta ba.

A zamansa na farko da manyan hafsoshin tsaro da na leken asiri da kuma shugaban ’yan sanda, Shugaba Bola Tinubu ya umarce su da su yi aiki tare domin cimma manufa guda, ta tabbatar da tsaro a fadin Najeriya.

“Tinubu ya umarci shugabannin tsaron da su hanzarta mika masa jadawalin da suka tsara na tabbatar da tsaron kasa, domin ba ya son bata lokaci kafin a magance matsalar,” kamar yadda Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguna, ya sanar.

Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana aniyarsa ta dorawa a kan nasarorin da aka samu a bangaren tsaro a zamanin magabacinsa, Muhammadu Buhari, ya bukaci shugabannin tsaron su rika daukar mataki da wuri a kan duk matsalar tsaro da ta taso, daga baya su gabatar da rahoto ga Kwamitin Tsaro na Kasa.

Ya kuma sanar da su cewa ya zama wajibi su hada kai wajen magance matsalar ta’addanci da ’yan bindiga da barayin danyen mai da ’yan fashin teku da dangoginsu da suka addabi kasar.

“Shugaban Kasa ya kuma ba da umarnin cewa dole sojoji su je duk inda ake fama da matsalar tsaro su magance ta, tare da ba su isassun kayan aiki da cikakken kwarin gwiwa da kuma kulawa da jin dadinsu yadda ya kamata.

“Hakazalika zai yi duk mai yiwuwa wajen samar wa hukumomin leken asiri duk abubuwan da suke bukata domin gudanar da aikinsu yadda ya dace kuma cikin sauki,” in ji Monguno.

Da yake sanar da su shirinsa na yin sauye-sauye da inganta harkokin tsaron kasa, Tinubu ya bukaci shugabannin tsaron da su gabatar masa da rahoto tare da tuntubar sa a-kai-a-kai, game da halin da ake ciki da kuma inda aka kwana.

Monguno ya shaida wa manema labarai cewa Shugaba Tinubu ya jaddada cewa bai kamata a bari wata matsala ta dankwafe Najeriya ba, a yayin da wasu kasashe ke samun nasarori.

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou