Umarnin kotu bai hana mu gudanar da kasuwancinmu ba – Kamfanin Dansa
Hukumar gudanarwar Kamfanin sarrafa kayan abinci da ruwan lemo ta Dansa Foods Ltd, ta bai wa abokan huldarta kwarin gwiwar ci gaba da hada-hadar kasuwancinsu, duk da cewa umarnin kotu ya hana bankuna ci gaba da hulda da kamfnain, inda Lauya Kamfnain, Mohammed Shitu Jibril ya bayyana umarnin kotu a matsayin cikas na ‘wucin gadi […]
Hukumar gudanarwar Kamfanin sarrafa kayan abinci da ruwan lemo ta Dansa Foods Ltd, ta bai wa abokan huldarta kwarin gwiwar ci gaba da hada-hadar kasuwancinsu, duk da cewa umarnin kotu ya hana bankuna ci gaba da hulda da kamfnain, inda Lauya Kamfnain, Mohammed Shitu Jibril ya bayyana umarnin kotu a matsayin cikas na ‘wucin gadi ne.’
A jawabin da ya yi wa manema labarai, ya bayyana cewa, “lauyoyinmu na dauakr duk matakan da suka dace don shawo kan matsalar, inda muka nuna rashin gamsuwarmu da umarnin kotu da kuma matakin da bankunan suka dauka.”
A makon da ya wuce ne, Mai Shari’a Okon Abang ya byar da umarni a makon da ya wuce, inda umarnin zai ci gaba da aiki har zuwa jiya Alhamis, 11 ga Satumbar 2014, inda kotun za ta duba karar da Bankin Union ya gabatar mata kan Shugaban Kamfanin Alhaji Sani dangote da kamfanoninsa.
Lauyan da ya ce, wannan matsalar ta kusa zama tarihi, nan ba da dadewa ba, inda ya bayyana cewa, wanda ake kara, da masu kara, duk za su zauna don warware matsalar, ta hanyar da kowa zai ji cewa an yi masa daidai, ba tare da tada jijiyar wuya ba.
Wannan kara da aka kai kamfanin Dansa da shuaban kamfanin, Alhaji Sani dangote, tuni lauyoyins asuka daukaka kara kan hukuncin toshe asusun ajiyarsa a Kotun Tarayya ta Legas a bayar da umarni, karkashin jagorancin Mai shari’a Okon Abang, a ranar 4 ga Satumbar 2014. An dai kai karar ne kan yadda Bankin Union ke korafin an ki biyansu bashin Naira biliyan biyar da kamfanin ya karba.