Ummu dankwambo ta sha alwashin kawar da yoyon fitsari kafin karshen badi

Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe Hajiya Ummu Adama Ibrahim dankwambo, ta ce burinta shi ne ta kawar da cutar yoyon fitsari a tsakanin matan jihar kafin karshen shekarar 2015 a kokrinta na tallafa wa matan jihar da kuma kula da lafiyarsu.Uwargidan Gwamnan ta bayyana haka ne a Gombe a lokacin da ta kai ziyarar ganin aikin […]

Ummu dankwambo ta sha alwashin kawar da yoyon fitsari kafin karshen badi
Ummu dankwambo ta sha alwashin kawar da yoyon fitsari kafin karshen badi

Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe Hajiya Ummu Adama Ibrahim dankwambo, ta ce burinta shi ne ta kawar da cutar yoyon fitsari a tsakanin matan jihar kafin karshen shekarar 2015 a kokrinta na tallafa wa matan jihar da kuma kula da lafiyarsu.
Uwargidan Gwamnan ta bayyana haka ne a Gombe a lokacin da ta kai ziyarar ganin aikin yi wa mata masu yoyon fitsari tiyata kyauta da ta dauki nauyi a Asibitin kwararru na Jihar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ta ce idan matan suka warke bayan tiyatar za ta sanya su a cikin shirinta na koya wa mata sana’o’in hannu mai suna (HAWEP). Ta ce rashin halartar mata masu juna biyu zuwa awon ciki saboda doguwar nakuda ke jawo cutar yoyon fitsari ga mata.
Uwargidan Gwamnan ta ce ganin akwai mazajen da suke hana matansu zuwa awo ya sa a shirin nata na HAWEP ta koya wa mata fiye da 100 aikin unguzoma saboda shiga karkara suna tallafa wa mata wajen karbar haihuwa.
Daga nan sai ta ce akwai wata kungiya da ba ta gwamnati ba, na wata ’yar was an fim mai suna Stephanie Okereke da ta nemi hada kai da Uwargidan Gwamnan don taimaka wa matan jihar masu fama da wannan cuta. Ta ce daga shekara ta 2012 da ta fara ba da wannan tallafi zuwa yanzu an samu yi wa mata 232 wannan aiki, inda a shekarar 2012 aka yiwa mata 56 a bara kuma an yi wa mata 76 sannan a bana an dauko mata 100 inda aka fara yi masu aiki.