Umura: Saudiyya za ta bayar da bizar kwana 15 ne kawai

kasar Saudiyya ta ce za ta fara takaita izinin zama a can don gudanar da aikin umura zuwa kwanaki 15 kacal, a wani mataki na rage cinkoson jama’a  a masallacin Harami.A ranar Talatar da ta gabata ne Ma’aikatar da ke Kula da Aikin Hajji a kasar ta bayyana wa jaridar al-Madinah  shirye-shiryenta na fara daukar […]

Umura: Saudiyya za ta bayar da bizar kwana 15 ne kawai
Umura: Saudiyya za ta bayar da bizar kwana 15 ne kawai

kasar Saudiyya ta ce za ta fara takaita izinin zama a can don gudanar da aikin umura zuwa kwanaki 15 kacal, a wani mataki na rage cinkoson jama’a  a masallacin Harami.
A ranar Talatar da ta gabata ne Ma’aikatar da ke Kula da Aikin Hajji a kasar ta bayyana wa jaridar al-Madinah  shirye-shiryenta na fara daukar matakin, inda kuma aka aike wa kamfanonin da ke aikin umura kudirin don neman ra’ayinsu cikin mako guda.
Har ila yau, ma’aikatar ta ce ta tattara korafe-korafan jama’a kuma ta fara shirye-shiryen fidda sabbin dokoki, wanda ake fatan matakin zai fara aiki zuwa karshen wannan shekarar. Wani mazaunin kasar ya bayyanawa jaridar Arab News cewa idan matakin ya tabbata zai taimaka wajen rage cinkoson jama’a a ciki da kewayen masallacin, wanda hakan zai kara bai wa masu ibada  natsuwa.
Kimanin mutane miliyan shida ne suka gudanar da aikin umura a lokacin watan Ramadan din da ya gabata. Kuma akwai mutum fiye da miliyan daya da dubu dari uku da za su gudanar da aikin hajjin bana, a cikin watan Oktoba mai zuwa.