Umurnin JAMB: Kishi ko kara kawo tabarbarewar ilmi?
Tun a wancan makon da Hukumar kula da shirya jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan wato JAMB, ta bada sanarwar kayyade irin yawan makin da irin wadancan manyan makarantu za su yi amfani da shi a bana wajen daukar dalibansu, wasu jama`a da kungiyoyi, musamman masu ruwa da tsaki a fannin ilmin kasar nan, su […]
Tun a wancan makon da Hukumar kula da shirya jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan wato JAMB, ta bada sanarwar kayyade irin yawan makin da irin wadancan manyan makarantu za su yi amfani da shi a bana wajen daukar dalibansu, wasu jama`a da kungiyoyi, musamman masu ruwa da tsaki a fannin ilmin kasar nan, su ka shiga mayar da martini akan makin ya yi kasa da yawa, kuma ba abinda hakan wai zai haifas, sai kara kawo tabarbarewar ilmin kasar nan, wanda su kace dama a tabarbaren ya ke.
Bayan dai wani taron masu ruwa da tsakiya a fannin ilmi mai zurfi da aka yi a wancan makon tare da Magatakardar Hukumar ta JAMB, Farfesa Is-hak Oloyede, ya fadawa taron manema labarai a Abuja cewa a bana an tsayar da maki 120, ya zama maki mafi kankanta da Jami`o`in kasar nan za su yi amfani da shi wajen daukar dalibansu, yayin da sauran manyan makarantu irin su Kwalejojin Ilmi da Kwalejojin Kimiyya da Fasaha aka kayyade masu makidari dari. Sabanin maki 180, da 160, bi da bi da manyan makarantun su ka saba amfani da su duk shekara.
Kodayake, tun a wancan taron manema labarai Magatakardar JAMB din, ya fadia musu cewa Majalisun Dattawan kowace jami`a da na gudanarwar sauran manyan makarantun, su ya kamata a barsu su yanke hukunci a kan abin da zai zama mafi kankantar makin da za su dauki dalibansu. Yana mai jaddada cewa ita Hukumar JAMB,abin da ta yi kawai shi ne yanke mafi kankantar makin da manyan makarantun gaba da Sakandaren su yi amfani da shi kamar yadda ta saba yi duk shekara.
A wajen wancan taro ne da Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu ya samu halarta, Ministan ya tabbatar wa jama`ar kasa da masu ruwa da tsakin cewa hanin da gwamnatin tarayya ta yi a bara na jami`o`i da sauran manyan makarantun na kar su gudanar da jarrabawar tantance wadanda za su dauka kamar yadda suka saba yi duk shekara, a bana an janye shi, hanin da gwamnatin tarayyar ta yi a barar ma an yi shi ne a kan kuskure.
A kan haka ya yi fatan manyan makarantun ba za su caji daliban da za su shirya ma jarrabawar, fiye da N2,000, ba. A bara dai Ministan ya hana manyan makarantun gudanar da jarrabawar ce bisa ga wai gwamnatin tarayya na zargin wasu manyan makarantun a kan sun mayar da gudanar da jarrabawar ta zama wata kafa ta cin hanci da rashawa.
Tun bayan fitar da waccan matsaya ta JAMB din, wasu `yan kungiyar Malaman jami`o`i, wato ASUU daga shiyya Kudu maso Yamma suka ce ba ta sabuwa wai bindiga a ruwa, har suna barazanar ba jami`ar da za ta yi amfani da wancan umurni da suka kira zai kara kawo tabarbarewar ilmi. Ita ma kungiyar dalibai ta kasa baki daya, wato NANS a wata ganawa da Kakakinta Bestman Okeafor ya yi da Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai wato NAN a Enugu a karshen makon jiya bayan, ta yi suka a kan rage makin shiga manyan makarantun, har barazana ta yi a kan cewa muddin Hukumar JAMB din ba ta sauya matsayinta ba a kan yawan makin da ta gindaya, to, kuwa ba makawa kungiyar ta NANS za ta yi kira da a soke Hukumar ta JAMB.
Sakatareen yada labaran kungiyar daliban na kasa baki daya da bai ambaci ranar da za su yi kiran a soke Hukumar ta JAMBdin ba, muddin ta ki canja matsayinta. Kazalika, NANS din ta ce rage makin ba abinda zai kara haddasawa sai tabarbarewar ilmi, wanda dama a fadarta a tabarbaren ya ke.
A zaman na ta martanin akan wadancan soke-soke da kiraye-kiraye akan umurnin da ta bayar, Hukumar JAMB din a karshen makon da ya gabata, a wata sanarwa da Kakakinta Dokta Fabian Benjamin, ya fitar ga manema labarai a Abuja, ta ce mummunan tsarin daukar dalibai a manyan makarantun kasar nan, kan tilastawa wasu dalibai neman guraben karo ilmi, walau a kasashen da su ka ci gaba ko anan nahiyar Afirka. Ya kawo misali da irin yadda a kasar nan idan dalibi na son ya karanta harshen Hausa, sai jami`o`in su ce sai yana da kiredit a darashin lissafi, alhali a Birtaniya, abin da kawai jami`o`insu su ke bukata akan wanda zai nazarci Hausar su ne kiredit a Hausa da Turanci.
Kakakin JAMB din ya ba da tabbacin cewa muddin Hukumomin manyan makarantun kasar nan za su bi ka`idojin da Hukumar ta JAMB da na Hukumar kula da Jami`o`i wato NUC da na Hukumar kula da Kwalejojin Kimiyya da Fasaha ta NABTE suka gindaya musu na tsayawa a kan ba da guraben karatu a yankunan da kewayen da suke da bin cancanta da dacewa da kuma la`akari da yawan maki da suka yanke wa kansu, to, kuwa za a samu guraben shiga manyan makarantun a kowane lungu da sakon kasar nan a jami`o`i da manyan makarantu 260, da ake da su mallakar gwamnatin tarayya da jihohi da sauran masu zaman kansu.
Hukumar ta JAMB, ta Kakakin na ta, ta tabbatar da cewa ko kusa ba tana nufin maki 120, da 100, su zama su ne ma fi kankanta wajen daukar daliban ba, da har dalibi zai ce da zarar ya samu yawan wadancan maki, to, kai tsaye zai shiga jami`a, ko wata babbar makaranta, tana mai ba manyan makarantun umurnin da su faro daga sama so yo kasa a kan yawan maki, wajen daukar daliban.
Ba ko shakka, kafin wannan karin bayani na JAMB, dole ne hankula su tashi, musamman daga wadanda suke begen ganin ingatuwar ilmi, don kuwa idan ka raba maki 120 gida hudu, hudun da ita ce yawan darasin da kowane dalibi kan rubuta kafin ya samu shiga jami`a ko wata babbar makaranta a kasar nan, za ka ga cewa zai tashi da maki 30, a kan kowane darasi, haka in ka raba 100, sau hudu zai ba ka maki 25, alhali ba wata jarrabawar karatun boko da aka taba cewa idan dalibi ya samu maki 30, balle 25, da za a ce ya ci wannan jarrabawar.
Amma yanzu da wannan bayani, Ina fatan wadanda aka dora wa alhakin ba da guraben shiga manyan makarantun za su sanya tsoron Allah da kishin mutanensu, su bi wannan sabon umurni na JAMB din, don Allah don son AnnabinSa, kar su bari rashin kishin mutanensu da son kudi da ribbatar shaidan su kwashe su, har su yi watsi da wannan tsari. Ni kam daga gare ni wannan sabon tsari kishi ne daga mahukuntan Hukumar ta JAMB na wannan zamani, Allah kuma Ya saka musu da mafificin alkherinSa.
Daga karshe, ina yi wa dukkan al`umman Musulmin duniya BARKA DA SALLAH da fatan Allah Ya sa Alhazai su kammala aikin Hajjin bana lafiya su kuma dawo kasashensu da gidaddajinsu lafiya, Amin summa amin.